Latest
Karamin ministan tsaro a Najeriya, Bello Matawalle ya tsoma baki kan batun hana sojojin Najeriya 'visa' zuwa kasar Canada inda ya ce za su dauki matakin da ya dace.
Mai girma shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya mika sakon ta'aziyya bisa rasuwar jagoran ƙungiyar yarbawa ta ƙasa watau Afenifere, Ayodele Adebanjo.
Mai magana da yawun APC reshen jihar Imo, Cajetan Duke ya bayyana cewa ba zai ci gaba da magana kan ra'ayoyin jam'iya ba, ya miƙa takardar ajiye aiki nan take.
Bayan korafe-korafen al'umma kan shirin 'Qur'anic Convention', rahotanni sun tabbatar da cewa an ɗage taron da aka shirya yi a Abuja cikin mako biyu.
'Yan majalisar dokokin Kaduna sun sauya sheka daga PDP zuwa APC saboda nasarorin Gwamna Uba Sani, suna mai alkawarin ci gaba da kawo zaman lafiya da ci gaba a jihar.
Hon. Philip Agbese ya musanta hannu a zargin neman na goro daga jami'in kamfanin kudin crypto watau Binance, ya ba Tigran Gambaryan kwana 7 ya janye.
Bayan caccakar Canada da Nuhu Ribadu ya yi, ofishin jakadancinta a Najeriya ya mayar da martani kan rahotannin hana hafsan tsaron Najeriya shiga kasar.
Tsohon Sanata, kuma tsohon magidanci Nasir El Rufa'i ya shawarci tsohon gwamnan Kaduna da ya nemi afuwan mutanen da ya jagoranta saboda zargin shiga hakkinsu.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa akwai tsananin talauci a Arewa maso Gabas, wanda ke bukatar a yi kokarin warware matsalar don ceto mutanen yankin.
Masu zafi
Samu kari