Latest
Rahotanni da muka samu sun ce rigima ta sake kunno kai a masarautar Zazzau bayan majalisar dokokin Kaduna ta karɓi ƙorafin cire Sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli.
Dembele da Lamine Yamal su ke kan gaba a jerin ƴan wasan da ka iya lashe kyautar gwarzon ɗan wasa ta Ballon d'Or ta bana bayan taka rawar gani a kakar 2024/2025.
Yayin da ake yawan auren matan Kenya, shugaban ƙasar, William Ruto, ya koka kan yadda 'ya'yansu mata da dama na auren maza 'yan Najeriya babu shiri.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka wasu daga cikin kwamnandojin kungiyar ISWAP a jihar Borno. An hallaka su ne yayin wata musayar wuta.
Tsohon gwamnan Rivers kuma ministan birnin Abuja, Nyesom Wike, ya musanta rahoto kan zargin ana juya akalar gwamnatin Shugaba, Bola Ahmed Tinubu.
Wani sanannen ɗattijon kasa daga Arewa, Alhaji Dabo Sambo ya bayyana cewa ba abin da ya fi ci wa ƴan Najeriya tuwo a kwarya kamar matsalar tsaro, ya gargaɗi Tinubu.
A labarin nan, za a ji cewa tsohon Sarkin Gwandu, Al-Mustapha Jokolo ya ce ya rungumi kaddara bayan kotun koli ta tabbatar da raba shi da sarautar Gwandu baki daya.
Jami'an yan sanda biyu sun rasa rayukansu yayin da wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai hari wurin hakar ma’adinai a Oreke-Oke-Igbo, jihar Kwara.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar dakile wani hari da mayakan ISWAP suka kai a jihar Borno. Sojojin sun hallaka 'yan ta'adda tare da kwato makamai.
Masu zafi
Samu kari