Shahararrun Jaruman Kannywood 5 Da Suka Taba Yin Soyayya Da Juna

Shahararrun Jaruman Kannywood 5 Da Suka Taba Yin Soyayya Da Juna

Jaruman fim suna daukar lokaci tare lokatan shirya fim, wanda hakan ke jawo abota ko kulluwar zazzafar soyayya.

Baya ga fitowa a matsayin ma'aurata ko masoya a fim, da yawan jaruman kan yi soyayya a zahiri, kamar yadda ake gani a fina-finan.

Rakiya Moussa
Jaruman Kannywood 5 da su ka taba soyayya da takwarorinsu. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

A Kannywood, masana'antar fina-finan Hausa a Arewacin Najeriya, akwai labaran jarumai da suka fada soyayya da abokan aikinsu da dama.

Wasu akan kai ga aure, amma wasu suna katsewa kafin a kai matakin.

Daily Trust ta zaklo wasu daga cikin jaruman Kannywood da suka yi soyayya amma ta lalace daga baya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Fati Washa da Zango

Fati Washa da Zango
Fitattun Jaruman Kannywood 5 Da Suka Taba Yin Soyayya Da Juna. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Fatima Abdullahi, da ta fi shahara da Fati Washa, na daya daga cikin jarumai mafiya sanuwa a Kannywood. Haifaffiyar Bauchi ce, ta fara fim kusan shekara 10 da su ka wuce, ta yi fina finai sanannu kamar Yar Tasha, Hisab, Farida da kuma shirin Labarina mai dogon zango.

Kara karanta wannan

Ga irinta nan: Yadda aka yiwa masu kwacen waya 2 a Kano hukunci mai tsanani a kotun Muslunci

Jarumar mai shekara 30 ta taba soyayya da daya daga cikin manyan jaruman masana'antar, Adam A. Zango, jarumi kuma mai shirya fim, cike da zazzafar soyayya da ta kusa kaiwa ga aure.

Rahoto ya bayyana sun bata bayan shafe shekara hudu ana soyayya. Tun bayan nan, Zango ya yi aure tare da sakin wasu mata biyu daban, amma ba a sake jin labarin soyayyar Washa ba.

Nafisa Abdullahi

Nafisa Abdullahi
Adam A Zango da Nafisa Abdullahi. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Nafisa ita ma babbar jaruma ce wadda ake matukar rububi a Kannywood. Haifaffiyar Jos din ta lashe lambobin yabo da dama, ta kuma yi fina-finan Nollywood.

Bayan sun yi fina-finai da dama da abokin sana'arta, Adam A. Zango, ko dai a matsayin masoya ko ma'aurata, zafafan hotunan jaruman ya cika shafukan sada zumunta don nuna irin alaka mai karfi da ke tsakanin jaruman, kafin daga bisani a fahimci soyayya su ke.

Daga baya Zango ya bayyana cewa sun shafe shekara uku su na soyayya kuma ya na da niyyar aurenta kafin kaddara ta gifta, wanda ke nufin an rabu.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Umarci Shettima Ya Fito da Tsarin Taimakon Talaka Bayan Janye Tallafin Fetur

Ya ce:

"na so Nafisa sosai kuma mun kusa yin aure kafin mu rabu."

Fati Muhammad

Fati da Ali Nuhu
Fati Muhammad da Ali Nuhu. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Fatima Muhammad tsohuwar jaruma ce da ke cikin mafiya dadewar jarumai mata a Kannywood, ta shafe sama da shekara 20 a masana'antar.

Ta yi fitattun fina-finai kamar Sangaya, Zarge da Marainiya, kafin ta auri jarumin fim, Sani Musa Mai-Iska, ta kuma koma birnin London, duk da auren ya mutu bayan wasu shekaru.

Sai dai, alakarta da babban jarumi, Ali Nuhu, ya sanya masoyanta na ganin cewa jarumi Ali Nuhu ya so aurenta kafin da hadu da Sani Musa Mai Iska ta aure shi.

Da ta ke sharhin maganar, ta ce tabbas suna da alaka mai kyau da Ali Nuhu, kuma sun taba soyayya da Ali Nuhu amma ba su shirya yin aure ba.

"Ka san aure da mutuwa abu ne a hannun Allah, duk da alaka ta da Ali Nuhu, na auri wani daban. Amma duk da haka Ali dan uwa ne a wajena." ta fada a wata hira.

Kara karanta wannan

Wasu Mahara Sun Harbe Fitaccen Farfesa a Jami'ar Najeriya Har Lahira, Sun Aikata Wani Abu Daban

Zainab Indomie

Adam A Zango da Zainab Indomie
Adam A Zango da Zainab Indomie. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Zainab Abdullahi, da aka fi sani da Zainab Indomie hazikar jaruma ce da ta fito a shahararrun fina-finai kamar Garinmu da Zafi, Yar Agadez da kuma Ga Duhu Ga Haske.

Ta bayyana cewa sun taba soyayya da jarumi Adam Zango a farkon shigarta masana'antar, tun da shi ne ubangidanta. Amma a 2014, ya sanar da baikonsa da wata matar da ba jaruma ba ce.

Rakiya Moussa Poussi

Rakiya Moussa
Rakiya Moussa Poussi da Hamisu Breaker. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Rakiya Moussa Poussi jaruma ce mai tasowa yar asalin kasar Niger da ta fara shahara saboda kwarewarta a rawa da ake gani a bidiyon wakokin Hamisu Breaker, Garzali Miko da Umar M. Sharif.

Ta janyo wata zazzafar muhawara a Arewacin Najeriya ga masu amfani da kafafen sada zumunta bayan wata tattaunawa da ta yi a wani shiri da fitacciyar jaruma Hadiza Gabon ke gabatarwa.

Batun Rakiya ya zama daya daga cikin wanda aka fi magana akai bayan ta bayyana abun da ke tsakaninta da wani mawakin Kannywood cikin kuka saboda gudunta da ya yi.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Dalilai 5 Da Yasa Yajin Aikin NLC Kan Man Fetur Ba Zai Yi Nasara Ba

Duk da ba ta bayyana suna ba, ta ce shahararren mamaki ne kuma tuni wasu ke alakanta ta da Hamisu Breaker, mai wakar Jarumar Mata.

Jarumar ta ce ba za ta daina son shi ba, kuma ta na tsoron auren wani, saboda tsohon masoyin nata ya na ranta har abada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel