Kotu Ta Garkame Malamin Addini da Matarsa Saboda Babban Laifi 1 da Suka Aikata

Kotu Ta Garkame Malamin Addini da Matarsa Saboda Babban Laifi 1 da Suka Aikata

  • Mai shari'a Adeola Olatubosun ta kotun majistare dake Sabo-Yaba, jihar Legas ta tura wani malamin addini da matarsa magarkamar Ikoyi
  • Ana zargin Fasto Azuka Ohez da matarsa, Mary Ohez da zambar kudade da yawansu ya kai naira miliyan 33.8 mallakin wani kamfanin mai
  • An rahoto cewa ma'auratan sun hada kai da wasu mutane da suka tsere wajen karbar kaso daga kudaden da aka samu ta hanyar damfara

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Lagos - Wata kotun majistare dake yankin Sabo-Yaba a jihar Legas, ta tura fasto na cocin 'Kingdom Power International Christian Praying Centre Ishashi', Azuka Ohez da matarsa, Mary Ohez magarkama.

An gurfanar da ma'auratan ne a ranar Laraba, 7 ga watan Fabrairu bisa zarginsu da hannu wajen damfarar wani kamfanin man shafa kudi naira miliyan 33.8, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Kotu ta ɗibawa Tinubu wa'adin kawo ƙarshen matsalar tsadar rayuwa a Najeriya

Kotu ta garkame mata da miji kan zambar kudade
An Tura Malamin Addini da Matarsa Magarkama Kan Damfarar Naira Miliyan 33.8 Hoto: Thisday
Asali: Twitter

Wadanda ake tuhumar wadanda basu da takamaiman adireshin wurin zama suna fuskantar tuhume-tuhume biyu na hada baki da zamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani laifi malamin da matarsa suka aikata?

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya rahoto cewa an gurfanar da ma'auratan ne a cikin zauren kotun majistaren.

Mai shari'a a kotun, Adeola Olatubosun, ta yi umurnin cewa a tsare ma'auratan a gidan gyara hali na Ikoyi har zuwa lokacin da za a karbi belinsu.

Olatubosun ta bayar da belin su a kan kudi naira miliyan 10 kowannen su tare da masu tsaya masa guda biyu kowannen su.

Sannan ta dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 13 ga watan Mayu domin ci gaba da zama.

Yadda ma'auratan suka karbi miliyoyi ta hanyar zamba

Da farko, mai gabatar da kara, ASP Rita Momah, ta shaida wa kotun cewa mutanen biyu da wasu da har yanzu ba a san inda suke ba sun aikata laifin ne a ranar 13 ga Yuli, 2023 a Oba Ayoka St, Legas.

Kara karanta wannan

Zanga-zanga sun tada hankalin Gwamnati, Shugaban kasa ya dauki mataki a guje

Momah ta yi zargin cewa ma’auratan tare da wani Chijioke Ezekirian sun hada baki wajen sata da karbar kudade daga kamfanin 'Climax Lubricants' dake Legas.

Ta bayyana cewa ma’auratan sun karbi jimillar naira miliyan 33.8 daga wajen Chijioke Ezekirian. ta asusun banki.

Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa Momah ta ce laifukan sun ci karo da sashe na 328 (1) da na 411 na dokar laifuka ta jihar Legas, 2015.

Malami ya kwancewa fastoci zani a kasuwa

A wani labari na daban, Fasto Ejike Mbaka, shugaban cocin Adoration Ministry, Enugu, Najeriya (AMEN), ya yi iƙirarin cewa yawancin fastocin Najeriya suna bayar da bayanan ƙarya da yin mu'ujizar ƙarya domin samun kuɗi da ɗaukaka.

Babban limamin cocin Katolikan ya bayyana hakan a cocin da ke birnin Enugu, cikin ƴan kwanakin nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel