Hotuna da Bidiyoyin Yadda ‘Yan Kannywood Suka Yi Bikin Nadin Ali Nuhu Mukami a Gwamnatin Tinubu

Hotuna da Bidiyoyin Yadda ‘Yan Kannywood Suka Yi Bikin Nadin Ali Nuhu Mukami a Gwamnatin Tinubu

  • Manyan jaruman masana'antar shirya fina-finan Hausa, Kannywood sun nunawa abokin sana'arsu, Ali Nuhu karamci kan sabon mukamin da ya samu a kwanan nan
  • Jaruman sun hadu kwansu da kwarkwata a wajen bikin nadin da aka yi wa Ali a matsayin shugaban hukumar fina-finai ta Najeriya
  • An gudanar da shagalin bikin ne a ranar Talata, 6 ga watan Fabrairu a kasaitaccen wajen taro na otal din Transcorp Hilton

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Babban birnin tarayya, Abuja - A ranar Talata, 6 ga watan Fabrairu ne aka gudanar da wani gagarumin liyafa na bikin nadin fitaccen jarumin fim, Ali Nuhu, mukami a matsayin shugaban hukumar fina-finai ta kasa.

Kara karanta wannan

Zanga-zanga sun tada hankalin Gwamnati, Shugaban kasa ya dauki mataki a guje

Taron wanda aka gudanar a kasaitaccen otal din Transcorp Hilton ya samu halartan manyan 'yan gwamnati, 'yan fim da sauran masu fada aji.

Jaruman Kannywood sun yi shagalin nada Ali Nuhu mukami
Hotuna da Bidiyoyin Yadda ‘Yan Kannywood Suka Yi Bikin Nadin Ali Nuhu Mukami a Gwamnatin Tinubu Hoto: rahamasadau
Asali: Instagram

Wani mukami Tinubu ya ba Ali Nuhu?

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya nada fitaccen jarumin wanda ake yi wa lakabi da sarkin Kannywood, domin ya jagoranci hukumar fina-finai ta kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ali ya fito a fina-finan Nollywood da Kannywood sama da guda 500, kuma ya samu lambar yabo da dama a harkar fim kama daga matsayinsa na jarumi, darakta, furodusa kuma mai rubutu.

Manyan jaruman masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, sun yi wa abokin sana'ar tasu kara inda suka hallara wajen bikin kwansu da kwarkwata.

A wajen taron an gano manyan jarumai irin su Rahama Sadau, Nafisa Abdullahi, Hadiza Gabon, Maryam Booth, Hafsat Idris da sauransu.

Ga hotuna da bidiyoyin shagalin a kasa:

Kara karanta wannan

Labari da dumi-dumi: Bola Tinubu ya shigo Najeriya bayan shafe makonni 2 a Faransa

Ali Nuhu ya ziyarci Sarkin Kano

Bikin na zuwa ne yan kwanaki bayan Ali Nuhu ya ziyarci fadar mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero domin ya sanya masa albarka a wannan mukami da ya samu.

Jarumin ya kuma jinjinawa sarkin tare da godiya a gare shi bisa shawarwari da addu'o'in da ya yi masa.

Ali Nuhu, wanda shine shugaban hukumar fina-finai ta kasa a yanzu, ya kuma samu rakiyar wasu daga cikin abokan sana'arsa zuwa fadar sarkin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel