An Yi Babban Rashi a Kannywood, Fitaccen Jarumi Suleiman Alaƙa Ya Kwanta Dama
- Rahotanni sun bayyana cewa Allah ya yi wa fitaccen jarumin Kannywood Suleiman Alaƙa rasuwa a yau Litinin 22 ga watan Yuli
- Darakta kuma jarumi a masana'antar da ake ji da ita, Al-Amin Ciroma ne ya fitar da labarin sanarwar rasuwar Suleiman Alaƙa
- Legit Hausa ta tattaro sakonni ta'aziyya da jarumai da mawakan Kannywood suka aika na rasuwar daya daga cikinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Rahotannin da muke samu a yanzu na nuni da cewa, jarumi a masana'antar Kannywood, Suleiman Alaƙa ya kwanta dama.
Suleiman Alaƙa ya juma yana taka rawa a fina-finan Kannywood duk da cewa tauraruwarsa ba ta haska sosai ba, amma ya ba da gudunmawa sosai.
Jarumi Suleiman Alaƙa ya rasu
Mun fara samun labarin rasuwar Suleiman Alaƙa ne daga wajen darakta kuma jarumi Al-Amin Ciroma kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Al-Amin Ciroma ya ce:
"Innaa lilLahi wa innaa iLaihi raaji'un. Suleman Alaqa na Kannywood ya rasu, Allah jikansa da rahama amin."
An ruwaito cewa jarumi Suleiman, ya rasu ne a yau Litinin, 22 ga watan Yulin 2024.
Masana'antar Kannywood ta na jimami
Da muka leka shafukan jaruman Kannywood, mun ci karo da wallafar mawaka da wasu jarumai da suka mika sakon ta'aziyyarsu na rasuwar jarumi Suleiman Alaƙa.
Jarumi a shirin Labarina, Umar Gombe (Damtse) ya fitar da sanarwar rasuwar Suleiman a shafinsa na Instagram inda ya yi addu'ar Allah ya jikan mamacin.
Umar Gombe ya ce:
"Allah ji kan Sulaiman Alaka, ya jaddada rahama ga iyayenmu ya sa mu cika da imani. Amin"
Jaruma ayshatulhumairah ta ce:
"Wayyo Allah mutumin kirki.
"Ubangiji Allah ya gafarta masa, Allah yasa mutuwa hutu ce da rahma a gare shi da dukkanin 'yan uwa da suka riga mu gidan gaskiya Allah ya yafe mana ya kyautata karshen mu"
Darakta aleegumzak ya ce:
"Allah ya gafarta masa ya sa ya huta."
Mawakiya official_hairat11 ta ce:
"Allah ya yi masa rahama amin."
Darakta hassan_giggs ya ce:
"Allah ya jikansa da rahama, amin."
Jaruma official_ummahshehu ta ce:
"Inna lilLahi wa’inna iLaihir raju’un, ya Allah ya jaddada rahama a gareshi."
Nafisa ta magantu kan masu zaginta
A wani labarin, mun ruwaito cewa jarumar Kannywood, Nafisa Abdullahi ta harzuka da irin yadda wasu mabiyanta ke fada mata bakaken maganganu a intanet.
Bayan sun kaita makura, jaruma Nafisa Abdullahi ta ware lokaci inda ta rika mayar masu da martani dai dai bakar maganar da suka yi mata.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng