"Ku Kyale Ta Kawai, Kowa da Kabarinsa", Sabon Hoton Rahama Sadau Ya Tayar da Kura

"Ku Kyale Ta Kawai, Kowa da Kabarinsa", Sabon Hoton Rahama Sadau Ya Tayar da Kura

  • Fitacciyar jaruwar masana'antar Kannywood, Rahama Sadau ta saki sabbin hotunanta zafafa da dandalin sosohiyal midiya
  • Wani mai amfani da shafin X @Sir_RomanticGuy ya haddasa cece-kuce bayan ya wallafa hoton Rahama tare da tambayar Musulma ce ko Kirista
  • Yayin da wasu ke ganin shigarta bata dace ba a matsayinta na Musulma, wasu na ganin babu ruwan shigar mutum da addininsa

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Fitacciyar jarumar Kannywood na Nollywood, Rahama Sadau ta saki sabbin zafafan hotunanta a dandalinta na soshiyal midiya.

A cikin hoton, jarumar ta yi shar da ita sanye sanye da bakar daguwar riga mai hannu daya, sannan kanta da kitson karin gashi.

Jaruma Rahama ta saki sabbin hotuna
“Ku Wayar Mun da Kai, Shin Kirista ce Ko Musulma?” Sabon Hoton Rahama Sadau Ya Tayar da Kura Hoto: rahamasadau
Asali: Instagram

Sai dai kuma, wani mai amfani da dandalin X mai suna @Sir_RomanticGuy ya kwafo hoton inda ya daura shi a shafin nasa.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da matar aure ta kama mijinta yana bacci da mahaifiyarta a jihar Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A saman hoton ya kuma yi wani tambaya wanda haddasa cece-kuce a tsakanin mabiya shafin nasa. Ya nemi a wayar masa da kai kan ko Rahama Musulma ce ko Kirista.

Ya rubuta:

"Ku wayar mun da kai don Allah, shin Kirista ce ita ko Musulma.....?"

Jama'a sun bayyana ra'ayoyinsu inda wasu ke ganin sam shigar tata bata dace da na Musulma ba wasu kuma na ganin babu ruwan addini da shigar mutum.

Martanin jama'a kan shigar Rahama Sadau

Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin martanin jama'a kan shigar jarumar a kasa:

@Sir_RomanticGuy ya ce:

"Allah ya shiryeta, Allah shi kaɗai ke shiryarwa muna Mata fatan shiriya."

@Ummieey_k ta yi martani:

"Ku kyale ta kawai, kowa da kabarin sa."

@HauwauOmar ta ce:

"'Yar uwa Musulma ce."

@Farouq__SG· ya yi martani

"Musulma ce kuma muna son ta."

Kara karanta wannan

Mai ba Jonathan shawara ya nunawa Tinubu hanyar farfado darajar Naira kan Dala

@iamolajide_ ya ce:

"Tabbass ta fara wuce gona da iri."

@Iam_Nafiu ya ce:

"Shagali kawai."

@yusufadantula ya ce:

"Kowa yasan be kamata musulmi suna wannan shigar b Amma sai suna goyon bayanta Kuma dukkansu d dalilan su .
"Kuma kowa yasan idan kaga musulmi Yana abun d Bai dace ba yakamata a fada musu gaskiya."

@abdullahimasho7 ya ce:

"Musulma ce amma ta bayyana a cikin shiga da bai dace ba wanda ya saba koyarwar Musulunci.
"Muna rokon Allah ya yi mata jagora sannan ya daura ta kan hanya madaidaiciya."

Sabon hoton Hadiza Gabon ya tada kura

A wani labarin kuma, fitacciyar jarumar Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon Aliyu Gabon, ta mayar da hankali wajen rage kibar da take da shi.

Sauyawar da ta yi zuwa yar ramammiya ya sanya mutane yin cece-kuce a dandalin soshiyal midiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel