Jarumar Kannywood Hadiza Gabon Ta Maka Wani Mutum a Kotu Kan Bata Mata Suna

Jarumar Kannywood Hadiza Gabon Ta Maka Wani Mutum a Kotu Kan Bata Mata Suna

  • Jarumar Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon ta maka wani mutum mai suna Bala Musa a gaban kotun Kaduna
  • Gabon ta zargi Musa da janyo mata zagi a wajen jama'a tare da bata mata suna
  • Mutumin wanda ya kasance ma'aikacin gwamnati ya zargi jarumar da cinye masa kudi sannan ta ki cika alkawarin da ta dauka na aurensa

Jihar Kaduna - Fitacciyar jarumar Kannywood, Hadiza Aliyu, wacce aka fi sani da Hadiza Gabon, ta maka wani ma'aikacin gwamnati mai suna Bala Musa a gaban kotun majistare da ke zama a hanyar Daura, jihar Kaduna.

Gabon ta yi karar Musa ne a ranar Laraba, 1 ga watan Nuwamba kan zargin bata mata suna, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Jarumar wacce ta magantu ta bakin lauyanta, Mista Mubarak Sani, ta ce ta sha suka da kalamai marasa dadi daga jama'a saboda kagen da wanda ake kara ya yi mata.

Kara karanta wannan

Wike ya sha alwashin daukar tsattsauran mataki kan wasu gine-gine a Abuja, ya fadi dalili

Hadiza Gabon ta maka matashi a kotu kan bata mata suna
Jarumar Kannywood Hadiza Gabon Ta Maka Wani Mutum a Kotu Kan Bata Mata Suna Hoto: adizatou
Asali: Instagram

Ya kara da cewar mutane, musamman a soshiyal midiya sun kira Gabon da macuciya wacce ta ki auren Musa bayan ta gama karbe masa yan kudadensa wanda ta bayyana a matsayin karya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wanda ake karar ta bakin lauyansa, Mista Naira Murtala, ya karyata zargin da ake yi masa.

Alkalin kotun, Shamsudeen Sulaiman, ya tambayi lauyan mai kara kan ko suna da shaidu inda suka amsa cike da tabbaci.

Alkalin ya bayar da belin wanda ake zargin bisa sharadin cewa zai gabatar da mutane biyu da za su tsaya masa wadanda za su zama mazauna jihar Kaduna kuma dole su zama ma'aikatan gwamnati.

Ya dage zaman shari'ar zuwa ranar 15 ga watan Nuwamba domin masu karar su gabatar da shaidunsu, rahoton Peoples Gazette.

Me ya haddasa rigimar tun farko?

Tun da farko dai wanda ake karan ya shigar da karar jarumar a kotun shari'a mai lamba 1, Magajin Gari a watan Maris din 2022. Ya zargi jarumar da kin aurensa bayan ya bata kudi N396,000.

Kara karanta wannan

Shugaban NLC ya magantu kan yadda aka lakada masa duka a jihar Imo

Jarumar ta karyata batun sanin Musa, cewa bata taba haduwa ko yin magana da shi ba a baya sannan babu wata alaka tsakaninta da shi.

Lauyan wanda ya shigar da karar ya gabatar wa kotun takardar banki cewa wasu mutane hudu ne suka karbi kudin da aka ce an aika wa wacce ake kara.

Biyu daga cikin mutanen hudu, Fatima Abdullahi da Abdullahi Yusuf, sun yi ikirarin cewa su aminiya wacce ake kara da hadiminta ne.

Sun amsa laifinsu na yi wa jarumar sojan gona tare da karbar kudi da sunan ta, inda suka roki kotu ta gafarta musu.

Kotu ta nemi a biya Gabon 500k na bata mata lokaci

Bayan rokon da Murtala ya yi na mika shari'ar zuwa kotun shari'a ta gaba, alkalin wancan lokacin, Isiyaku Abdulrahman, ya kori karar sannan ya sallami Gabon a ranar 31 ga watan Oktoba.

Ya umarci lauyan mai kara da wanda yake karewa da su biya jarumar N500,000 saboda bata mata lokacinta.

Kara karanta wannan

Budurwa ta cire kunya ta nemi saurayi ya bata lamba, sun kusa aure

Jaruma Fati Muhammad ta dauki zafi

A wani labarin, mun ji cewa tsohuwar jarumar Kannywood Fati Muhammad ta fito ta yi martani a kan kwamet da wani ya yi mata a shafin soshiyal midiya.

Matashin dai ya yi kalamai masu sosa zuciya ga jarumar har ya kai ga danganta ta da maita da kuma kiranta da sauran Askarawa.

Fati ta ce ita bata taba bilicin ba domin tunda fara ce ita tas, sannan ta ce ba za ta taba yafewa mutumin ba sai Allah ya saka mata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel