Mai ba Jonathan Shawara Ya Nunawa Tinubu Hanyar Farfado Darajar Naira a Kan Dala

Mai ba Jonathan Shawara Ya Nunawa Tinubu Hanyar Farfado Darajar Naira a Kan Dala

  • Reno Omokri ya soki yadda hukumar NCC ta ba kamfanin MTN gata duk da daga kasar waje suke
  • Hadimin tsohon shugaban Najeriyar ya ba Bola Tinubu shawarar sake duba alakar MTN da gwamnati
  • Fasto Omokri bai ga dalilin da MTN zai rika karbar VAT ba sannan a kullum ya rika ficewa da Daloli

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Idan ana so a dawo da kimar Naira, Reno Omokri ya rubuta a shafinsa, sai an duba har yadda hukumar NCC ta ke aiki.

Hadimin na Goodluck Jonathan yana bada shawarar yadda za a samu saukin tashin da Dala ta ke yi a yau.

Dala:Omokri - Tinubu
Tashin Dala: Reno Omokri ya ba Bola Tinubu shawara Hoto: @Dolusegun16, @RenoOmokri
Asali: Twitter

Idan aka bi ta Reno Omokri, ya ce Najeriya za ta tsira da kusan $10bn yadda aka kubuta daga irin wannan asara a shari’ar P & ID.

Kara karanta wannan

Duk da suka daga 'yan Arewa ministan Tinubu ya dage kan mayar da FAAN zuwa Legas, ya fadi dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ra’ayin fitaccen marubucin, kusancin shugabannin NCC da kamfanin MTN ya yi yawa, ya jero wasu tambayoyi masu neman amsa.

Reno Omokri a kan batun Dala

"Me zai sa a ba MTN izinin karbar harajin VAT a matsayinsu na kamfanin sadarwa daga kasar waje?
"Me ya hada su da VAT? Su wanene shugabannin da ke kula da NCC da suka ba MTN ikon nan, a wani dalili?
"Wace alaka wasu shugabannin majalisar da ke kula da NCC suke da ita da kamfanin MTN?
"Shin sa’a aka ci da wasu manyan jami’an hukumar FIRS suke cikin wannan majalisa (ta hukumar NCC)?"

- Reno Omokri

Omokri yace a shigo da EFCC

"Ya kamata hukumar EFCC ta duba lamarin. Wannan cin amana ne da kuma rashin adalci.
"A Amurka, kamfanoni da yawa da suka yi wannan sun gamu da takunkumi da tarar biliyoyin daloli, kuma wasu sun tafi gidan yari."

Kara karanta wannan

EFCC ta gano kungiyar addini da ke taimakon ‘yan ta’adda

- Reno Omokri

A rubutunsa a X, Omokri ya ambaci sunayen irinsu Ernest Ndukwe wanda yake NCC da tsohon Minista, Omobola Olubusola Johnson.

Dala ta doshi N1500 a BDC

Yayin da Dala ke ta tashi, Omokri ya zargi MTN da Airtel da sanadiyyar da Dala miliyan 20 ke barin Najeriya zuwa ketare a kullum.

Bankin CBN ya sanar da cewa an gama biyan bashin da kamfanonin jiragen sama su ke bi, ana sa ran samun dalolin da za a saki a kasuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel