“Allah Ya Raya”: Jarumi Abale Ya Samu Karuwar ’Ya Mace, Kannywood Ta Amsa

“Allah Ya Raya”: Jarumi Abale Ya Samu Karuwar ’Ya Mace, Kannywood Ta Amsa

  • Shahararren jarumi a masana'antar shirya fina-finan Hausa, Daddy Hikima, ya samu karuwar diya mace, ya wallafa hotunanta a shafin sa na Instagram
  • A ranar 27 ga watan Janairun wannan shekarar ne aka dauka auren jarumin da masoyiyarsa Maryam, auren da ya samu halartar manyan jarumai
  • Bayan wallafa sanarwar samun karuwar, jarumai a masana'antar da masoyansa sun yi tururuwar taya shi murna da yi wa yarinyar addu'a.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kano - Jaruminin Kannywood, Adam Abdullahi Adam, wanda aka fi saninsa da Daddy Hikima, ko Abale a fina-finan Hausa, ya samu karuwar kyakkyawar diya mace.

Jarumin ya sanar da hakan a shafinsa na Instagram, a ranar Juma'a, 17 ga watan Nuwamba, inda ya dora hoton kyakkyawar yarinyar, inda ya yi mata addu'a tare da sanya mata albarka.

Kara karanta wannan

Dakarun Najeriya sun kama ’yan ta’adda 122, sun ceto mutane 189 cikin mako daya, DHQ

Jarumi Daddy Hikima
Jaruman Kannywood da suka hada da, Ali Nuhu, Rahama Sadau, Momy Gombe, da sauran su, sun taya Abale murnar samun karuwa Hoto: @daddyhikima
Asali: Instagram

Daddy Hikima, ya rubuta cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Masha Allah. Allah ya azurtani da samu karuwar 'ya mace. Allah yarayata cikin imani da tarbiyar addinin musulunci.
Barka da zuwa wannan duniyar 'yar diya ta AMMI."

Ga abin da jarumin ya wallafa:

Kamar suna jira, jarumin na wallafa hoton da sanarwar, masoya da abokan sana'arsa suka fara tururuwar sanya wa diyar albarka da yi masa murna.

Jarumin Kannywood, Ali Nuhu, ya yi martani karkashin wallafar Abale, yana cewa:

Ina taya ka murna, tare da yi maka maraba da shigowa kungiyar iyaye.

Jaruma Rahama Sadau kuwa, cewa ta yi:

"Masha Allah … Allah ya raya "

Daraktan fina-finan Hausa, Falalu A Dorayi, ya ce:

"Ina taya ka murna daddy. Allah yai mata albarka."

Babban mai shirya fina-finan Hausa, Bashir Mai Shadda, ya taya jarumin murna, inda ya ce:

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Alkali ya umurci a bai wa Emefiele masauki a gidan yarin Kuje

"ALHAMDULILLAH ❤️❤️❤️❤️❤️ Ina taya ka murna"

A ranar 27 ga watan Janairun wannan shekarar ne jarumin ya angwance da amaryarsa Maryam Faruq Sale, kamar yadda mujallar fina-finan Hausa ta wallafa.

Ali Nuhu, Maryam Booth, Umar M. Sharif da sauransu suka wallafa tare da masa fatan alheri a shafukan su na Instagram, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Samun karuwar diya mace yanzu zai kara wa jarumin kwarjini da daraja a cikin jama'a, tare da mayar da shi mahaifi wanda zai kasance mai daukar sunan "uba".

"Masha Allah Allah yaraya "

Sakon jaruma Momy Gombe.

Jarumi Abdul M Shareef shi ma ya taya jarumin murna:

"Ina taya ka murna malam. Allah ya raya mana ya Kuma ba uwar lafiya"

Jarumi Abale, ya kasance daya daga cikin jaruman da ke shuhura a masana'antar shirya fina-finan Hausa, wand akuma ya taka rawa a manyan shirye shirye irin su; Sanda, dan jarida, gidan sarauta, a duniya, da sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel