Netflix: Jaruma Rahama Sadau Ta Ciri Tuta, Ta Kafa Babban Tarihi a Shirin Fim Na Kannywood

Netflix: Jaruma Rahama Sadau Ta Ciri Tuta, Ta Kafa Babban Tarihi a Shirin Fim Na Kannywood

  • A karon farko, shirin fim na masana'antar shirya fina-finan Hausa watau Kannywood zai shiga manhajar Netflix
  • Za a fara haska fim ɗin Hausa mai suna 'Mati a Zazzau' wanda Rahama Sadau ta shirya a Netflix ranar Asabar 30 ga watan Disamba
  • Fim ɗin ci gaba ne na shirin 'Mati da Lado' wanda shi ma fitacciyar jaruma, Rahama Sadau ce ta shirya shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

A karon farko, fim ɗin Hausa na masana'antar shirya-shirya fina-finan Hausa watau Kannywood zai shiga manhajar haska fina-finai Netflix.

Fim ɗin mai suna, 'Mati a Zazzau" zai zama fim ɗin Kannywood na farko da za a fara haskawa a Netflix.

Kara karanta wannan

'Dan takarar gwamnan kuma sanata ya bayyana shirinsa na sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC

Mati a Zazzau.
Kannywood: A karon farko, za a fara haska fim ɗin Hausa a Netflix Hoto: Rahama Sadau
Asali: Twitter

Shirin wanda fitacciyar jarumar nan ta Kannywood, Rahama Sadau, ta shirya za a fara haska shi a manhajar Netflix yau Asabar, 30 ga watan Disamba, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahama Sadau, shararrriyar jaruma wacce ke fitowa a fina-finan Kannywood da Nollywood ta kudancin Najeriya ce ta tabbatar da haka a shafinta na tuwita.

Da take tabbatar da ci gaban, Rahama Sadau ta rubuta a shafukanta na kafafen sada zumunta cewa:

“Mati a Zazzau zai zo muku a Netflix daga ranar 30 ga Disamba, 2023. Fim ɗin farko daga masana'antar Kannywood a kan Netflix."

Takaitaccen bayani kan fim ɗin Mati a Zazzau

Shirin ‘Mati A Zazzau, wanda Rahama Sadau ta shirya kuma Yaseen Auwal ya bada umarni, zai fito a karon farko, da mawakiyar Marvin Hadiza Blell, wacce aka fi sani da Di’Ja, a Kannywood.

Kara karanta wannan

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, tsohon shugaban ICAN kuma fitaccen ɗan kasuwa a Najeriya ya mutu

Fim din dai ci gaba ne na wani fitaccen shirin Kannywood mai suna ‘Mati da Lado’ shima na Rahama Sadau.

A cikin shirin, Mati ya koma birnin Zazzau ba tare da wani kwakkwaran dalili da nufin zama a can ba, amma sai ya gano cewa marigayi mahaifinsa ya mutu ya bar dukiya mai tarin yawa.

Sakamakon haka ne Mati ya lashi takobin kwato kuɗin da mahaifinsa ya bari ta ko wane hali, duk rintsi duk wuya.

Rahama Sadau ta yi bikin cika shekara 30

A wani rahoton na daban Jarumar Kannywood da Nollywood Rahama Sadau ta cika shekaru 30 da haihuwa, ta yi kalamai masu ratsa zuciya.

A ranar 7 ga watan Disamba 1993 aka haifi Rahama Sadau a jihar Kaduna, kuma ta fara shuhura a fim a shekarar 2013.

Asali: Legit.ng

Online view pixel