Kan Ta Waye: Yadda Aka Cinye Kudi Na Da Sunan Za a Yi Min Fim a Kannywood, Jaruma Saudat

Kan Ta Waye: Yadda Aka Cinye Kudi Na Da Sunan Za a Yi Min Fim a Kannywood, Jaruma Saudat

  • Labari kan yadda ake kan ta waye a masana'antar shirya fina-finan Hausa ba bakon abu ba ne, jaruma Saudat Amin ta zo da na ta labarin
  • A cewar jarumar, ta sayar da sarkokin zinaren da aka ba ta lokacin aurenta don ta yi fim, amma a karshe aka cinye kudin
  • Batu kan jarumai mata da ke shiga Kannywood kuwa, jarumar ta ce wasu matan na shiga fim don bunkasa sana'ar karuwancinsu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kano - Jaruma a Kannywood, Sa'adat Aminu, wacce aka fi sani da Saudat Amin, ta ce ba ta shiga Kannywood da kafar dama ba, saboda kan ta waye da aka yi mata.

Kara karanta wannan

Kannywood: “Zan biya gaba daya bashin da ake bin Amunu S Bono” – Aisha Humaira

Saudat wacce 'yar asalin kasar Nijar ce, ta tariyo yadda ta nemi izinin iyayenta ta je Kano, don shiga fim, inda aka hada ta da kanin 'yar uwarta don ya yi mata jagora.

Jaruma Saudat Amin ta fadi wasu abubuwa da ke faruwa a masana'antar Kannywood
Jaruma Saudat Amin ta ce ita nata kan ta wayen mai sauki ce yayin da ake fasikanci da wasu don a sanya su a fim. Hoto: FreedomRadioNigeria
Asali: Facebook

Ni ma an yi mun kan ta waye a Kannywood, Jaruma Saudat

A cewar ta, ta sayar da sarkokin zinaren da aka ba ta lokacin aurenta, ta tatta kudin ta ba kanin 'yar uwar da sunan zai yi mata fim, daga baya ta gano ashe an dade da yin fim din.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da hakan, jarumar ta ce nata da sauki, akan matan da ake yi masu kan ta waye ta fuskar yin fasikanci da su kafin a sanya ta a fim.

"Wasu idan suka fahimci ke ballagaza ce, sai su nemi budurcin ki", a cewar Jaruma Saudat.

A zantawarta da gidan rediyon Freedom da ke Kano, Saudat ta ce akwai gaskiya a kalaman da mawaki Abdullahi Amdaz ya yi kan halayen wasu jarumai a masana'antar ta Kannywood.

Kara karanta wannan

'Ba zan taba fitowa a fim da ya ci mutuncin al'adar Hausawa ba', Aisha Najamu

Dalilin da ya sa mata ke shiga Kannywood - Saudat

Jarumar ta ce:

"Duk wata yarinya da ka gani a Kano sai ta ce maka yar fim ce, dole a tantance wadanda ke shiga fim, a san dalilin zuwansu masana'antar don fitar da bara gurbi."
"Akwai matan da ke shiga fim don bunkasa karuwancinsu, ta yadda manyan mutane za su sansu, su rinka zuwa kasashen waje suna barikinsu, abinda ke kawo su kannywood kenan."
"Akwai wacce kuma ta duba yanayin kyawunta da dirinta, ta ga ya dace ta shiga fim, kuma za ta samu kudi ta rufawa kanta asiri, shi ma wannan dalili ne ga wasu."

Ko da aka tambaye ta kan dalilin da ya sa ba ta amsa gayyatar da hukumar Hisba ta yi wa 'yan fim ba, Saudat ta ce ba ta kasar ne, ta je bikin kanwarta.

Ana tallata karuwanci a Kannywood

A baya ne Legit Hausa ta ruwaito maku yadda hukumar tace fina-finai da dab'i ta jihar Kano ta dakatar da jarumi Abdul Saheer, kan wani bidiyo da ya wallafa a shafin TikTok.

Kara karanta wannan

“Na zata ba zai yiwu ba”: Tsoho dan shekaru 87 ya fada tarkon son kawar diyarsa, ya yi wuff da ita

A zantawarsa manema labarai, shugaban hukumar, Abba El-Mustapha, ya ce sun sami jarumin da aka fi sani da Malam Ali a shirin kwana casa'in da wallafa bidiyo da ke yada badala.

Sai dai, mawaki Abdullahi Amdaz, ya amayar da abinda ke cikinsa kan halayen wasu jaruman masana'antar, inda ya ce ana tallata karuwanci a kannywood.

A hirarsa da gidan talabijin na Muryar Amurka (VOA), Amdaz ya furodusosin masana'antar ne ke tallata karuwanci, kuma ko gaban waye zai kara nanata hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel