"Akwai Kotun Allah": Martanin Jama'a Bayan Kotu Ta Yanke Hukunci a Shari'ar Abba Da Ado Doguwa

"Akwai Kotun Allah": Martanin Jama'a Bayan Kotu Ta Yanke Hukunci a Shari'ar Abba Da Ado Doguwa

  • Kotu ta yanke hukunci a shari'ar gwamnatin Kano da dan majalisar tarayya, Alhassan Ado Doguwa
  • Mai shari'a Donatus Okorowo ya kori karar gwamnan Kano tare da umurtansa da ya biya Doguwa diyyar naira miliyan 25
  • Yan Najeriya sun tofa albarkacin bakunansu kan hukunci, da dama sun ce akwai sauran kotu daya da baya bukatar lauyoyi a madakata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kano - A ranar Juma'a, 1 ga watar Disamba ne kotu ta yanke hukunci kan karar da Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya shigar, inda yake zargin Alhassan Doguwa da ta'addanci.

Da yake tabbatar da hakan a shafinsa na X, Doguwa ya bayyana cewa Mai shari'a Donatus Okorowo, ya soke umurnin Gwamna Yusuf na sake bitar shawarar doka daga Atoni Janar na jihar kan zargin kisan da ake masa a lokacin zabe.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Lauyoyin arewa fiye da 600 za su maka gwamnatin Tinubu a kotu, sun fadi dalili

Kotu ta mallakawa Doguwa diyyar miliyan 25
"Akwai Kotun Allah": Martanin Jama'a Bayan Kotu Ta Yanke Hukunci a Shari'ar Abba Gida da Ado Doguwa Hoto: : Hon Alhassan Ado Doguwa/Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Dan majalisar tarayyar ya kuma bayyana cewa kotun ta yi umurnin biyan diyyar naira miliyan 25 na bata suna da jefa Doguwa cikin kunci da Abba Gida Gida ya yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon shugaban masu rinjayen a majalisar wakilan ya kuma mika godiyarsa ga tawagar lauyoyinsa karkashin jagorancin Afam Osigwe, kan kokarin da suka yi na kare shi da tabbatar da nasararsa a kotu.

Ya kuma yi godiya ga daukacin jama'ar da suka mara masa baya a lokacin da yake cikin matsala.

Yan Najeriya sun martani kan hukuncin kotu a shari'ar Doguwa da Abba

Tuni mutane suka garzaya sashin sharhi domin tofa albarkacin bakunansu, inda wasu suka jaddadad cewar akwai kotun Allah a lahira.

@Ameenullahi__ ya yi martani:

"Da fatan kana da kwararrun lauyoyi da za su kare shari'arka a lahira?"

@jafarinde ya ce:

"Kotin Allah dai babu Mai shari'a Donatus Okorowo. "

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Lalong ya magantu kan barin majalisar Tinubu ko komawa majalisar dattawa

@MaifadaFarouk ya yi martani:

"A banza tinda akwai sauran kotu guda daya wacce bata bukatar lauya kuma alkalin ta guda daya ne , sannan baki baya bada shaida saidai sassan jiki. Kuma wallahil azeem sai mu riski wannan rana."

@tanimu91 ya ce:

"Ko anki ko anso wata rana mai zuwa nan kusa kujera dole zata zama tarihi babu dawwamamme indai nan gidan duniya ne. Alqalai kuma well done kuma akwai ranar da shari'a adala zata zo kanku ranar da dogon turanci bazai amfani mai gaskia ba ma, ballantana wanda yayi karya."

@MuhdSan65949850 ya yi martani:

"Ai baka sha ba. Sarkin yana madakata inda babu justice danatus. A nan ne zamu tabbatar da gaskiyarka."

@azhar_love_bird ya ce:

"Allah Yana Nan Yana jiran Azalumai "

@aman854 ya ce:

"Akoi kotun Allah nah jiranka Alaji."

@Zakiyyutwd ya ce:

"Na tayaka murna jagoranmu. Tabbas Gaskiya tayi halinta.
"Allah yaƙara kareka."

@YNuraab ya ce:

Kara karanta wannan

"Ina bakin ciki matuka": Gwamnan Kano ya yi alhinin mutuwar Asm'u Sani da kansa ta kashe

"Akwai kalo rana gobe kiyama, domin achan Allah ne xaiyi hukunci dakansa!!!"

@HussainiTj ya ce:

"Na Doguwa dan Ado, kaci burodi ka yaga leda"

@abkzabson ya ce:

"Allah yana gani wayenda suka rasu allah zaibi kadin hakkinsu koma waye gake da hannu a ciki baruwan allah da kotun duniya muddin batayi adalci ba."

Kano: Shehu Sani ya yi martani ga Doguwa

A wani labarin, Legit Hausa ta kawo a baya cewa tsohon dan majalisar tarayya Shehu Sani, ya yi martani ga furucin da aka ce tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya yi cewa cin zabe ba wai ga yawan kuri'un da aka kada bane kawai.

Da yake jawabi yayin wata hira a Channels TV a ranar Laraba, 29 ga watan Nuwamba, Doguwa ya ce cin zabe yana da nasaba da bin ka'idojin wasan, Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel