'Ba Zan Taba Fitowa a Fim da Ya Ci Mutuncin Al'adar Hausawa Ba', Aisha Najamu

'Ba Zan Taba Fitowa a Fim da Ya Ci Mutuncin Al'adar Hausawa Ba', Aisha Najamu

  • Jarumar fina-finan Kannywood Aisha Najamu ta yi magana kan irin rawar da ba za ta iya taka wa a fim ba
  • Aisha wacce aka fi sani da Aisha Izzar So ta bayyana cewa ba za ta iya fitowa a fina-finan da suka taɓa al'adar Hausawa ba
  • A cewar ta dole ne a matsayinta na jaruma ta yi taka tsan-tsan kafin ta fito a cikin fim domin guje wa yin abin da ya ci karo da al'adar mutanen Hausawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jarumar masana'antar fina-finan Kannywood, Aisha Najamu wacce aka fi sani da Aisha Izzar So, ta bayyana cewa ba za ta taɓa fitowa a fim ɗin da zai taɓa ƙimar al'adar Hausawa ba.

Kara karanta wannan

“Na zata ba zai yiwu ba”: Tsoho dan shekaru 87 ya fada tarkon son kawar diyarsa, ya yi wuff da ita

Jarumar ta bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa ta musamman da ta yi da jaridar Daily Trust.

Aisha Najamu ta magantu kan Kannywood
Aisha Najamu ta ce ba za ta fito a fim da ya ci mutuncin al'adar Hausawa ba Hoto: @official_aisha_izzar_so
Asali: Instagram

Aisha Najamu wacce haifaffiyar jihar Jigawa ce ta bayyana cewa da farko iyayenta, ba su so ta shiga harkar fim saboda maganganun da ake yaɗa wa a kan masana'antar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta bayyana cewa daga baya ta samu ta shawo kansu, kuma har yanzu ba ta yi abin da zai sanya su yi dana sanin barin ta shiga harkar fim.

Aisha Najamu ta magantu kan fitowa a fim

Da aka tambaye ta ko tana zaɓar fina-finai kafin ta yarda ta fito a cikinsu, sai ta kada baki ta ce:

"Ba batun yin zaɓe ba ne, amma batun yin taka tsantsan. Ku tuna fa muna yin fina-finan Hausa kuma muna da al’adu da ɗabi’u da ƙa’idoji na addini da za mu kare."

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda fuskar wata mata ta sauya gaba daya bayan wani ya taba ta a wajen birne gawa

"A matsayina na ƴar arewa kuma uwa, ni ma ina da sunana don kiyayewa da kariya, saboda haka, ba zan iya yarda da kowace rawa ba tare da bin rubutun ba.
A matsayi na, na ƴar Arewa kuma uwa, ina da mutunci na da ƙima ta da zan kare, saboda haka ba zai yiwu na yarda na taka kowace rawa ba, ba tare da na duba abin da labarin ya ƙunsa ba."
"Muna rayuwa ne a cikin al'ummar da yanzu ta ke karɓar sababbin abubuwa saboda haka ba za mu yi kasadar zubar da ƙimar ɗabi'un mu ba."
"Kamar yadda na faɗa a baya muna da ɗabi'u da zamu tallata tare da kare su, saboda haka dole sai na duba labarin domin tabbatar da cewa ina yin abin da ya dace. Ba zan taɓa fitowa a fim ɗin da ya ci mutuncin ɗabi'u da al'adun Hausawa ba."

Jarumi Abale Ya Samu Ƙaruwar Ɗiya Mace

Kara karanta wannan

“Ba zan daina sonka ba”: Matashiya ta nunawa duniya saurayinta dan wada

A wani labarin kuma, jarumin fina-finan masana'antar Kannywood, Adam Abdullahi Adam, wanda aka fi sani da Abale ya samu ƙaruwar ɗiya mace.

Jarumin ya sanar da samun ƙaruwar ne a shafinsa na Instagram inda ya ɗora hotunan kyakkyawar ɗiyar ta sa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel