"Yanzu Mayakan Boko Haram Shigar Mata Suke Yi Yayin Kai Hari" - Ndume

"Yanzu Mayakan Boko Haram Shigar Mata Suke Yi Yayin Kai Hari" - Ndume

  • Sanata Ali Ndume ya bayyana wasu dabaru da mayakan Boko Haram ke amafani da shi wajen kai hare-hare
  • Ndume ya ce yanzu mayakan kungiyar ta'addancin sun koma sanya tufafin mata yayin kaddamar da hare-hare a garuruwan Borno
  • Ya taya zababben shugaban kasa, Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima murnar cin zabe

Borno - Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan rundunar soji, Sanata Ali Mohammed Ndume, ya bayyana cewa yanzu mayakan Boko Haram shigar mata suke yi yayin kai hari kan garuruwa a jihar Borno.

Ndume ya bayyana hakan ne yayin zantawa da manema labarai kan sake zabansa a karo na biyar a majalisar dattawa.

Ya ce a kwanan nan, mayakan Boko Haram sanye da tufafin mata sun kai hari garinsa, inda suka kashe mutum daya tare da jikkata wasu biyar a ranar zabe, Nigerian Tribune ta rahoto.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: An Gurfanar da Ado Doguwa a Gaban Kotu, Babban Abinda Ake Zarginsa Ya Fito

Sanata Ali Ndume yana jawabi
"Yanzu Mayakan Boko Haram Shigar Mata Suke Yi Yayin Kai Hari" - Ndume Hoto: Vanguard
Asali: UGC

A cewarsa, yanzu rundunar soji na da kayan aiki idan aka kwatanta da abun da ya faru a baya inda mayakan Boko Haram suka kwace kananan hukumomi da dama a Borno.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa mayakan Boko Haram sun yi nufin hana zabe a yankin, suna masu harin wurare uku a Gwoza wadanda suka hada da ofishin INEC, makarantar Firamari na Gwoza da Ajari, rahoton The Sun.

Ndume ya ce:

"Muna godiya sosai da jarumtar rundunar soji da sauran hukumomin tsaro a Gwoza musamman kwamandan bataliyan da ya nuna jarumta.
"Ya dauke su tsawon awa daya ne kawai wajen daidaita lamarin, ina so na bayyana cewa a yanzu rundunar soji na da kayan aiki saboda na sha mamakin kayayyakin da suke da shi lokaci da suka fara barin wuta daga kan tsaunin sun yi nasarar samun wadanda suke hari daga inda suke.

Kara karanta wannan

"A Soke Wannan Zaben Ayi Sabon Lale" Kwamitin Kamfen Atiku Ya Yi Kira Ga INEC

"Yanzu Boko Haram na kera harburushin gargajiya, suna sanya tufafin mata wajen kai hari garuruwa kuma hakan ya shafi fitowar masu zabe a Gwoza."

Ndume ya taya Tinubu da Shettima murnar cin zabe

Sanatan ya taya Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da abokin takararsa Kashim Shettima murnar cin zaben shugaban kasa.

Ya bayyana babban zaben na 2023 a matsayin zabe na gaskiya da amana.

"Na san cewa akwai wasu matsaloli tattare da na'urorin BVAS a wasu wurare, amma mun gode Allah APC ta yi nasara," in ji shi.

Ndume ya kuma yi jaje ga wadanda gobarar kasuwar 'Monday Market' ya ritsa da su a Maiduguri, yana mai shan alwashin cewa gwamnatin tarayya za ta tallafa masu.

A baya mun kawo cewa mummunar gobara ta lakume babbar kasuwar 'Monday Market' da ke Maiduguri inda aka yi asarar miliyoyin nairori.

Asali: Legit.ng

Online view pixel