Tsohon Ministan Buhari da Tsohon Gwamna Su na Hangen Shugabancin Majalisar Dattawa

Tsohon Ministan Buhari da Tsohon Gwamna Su na Hangen Shugabancin Majalisar Dattawa

  • Wadanda suka sake lashe zaben Majalisa sun fara yi wa sababbin-zuwa kamfe domin samun mukami
  • Ana tunanin Godswill Akpabio da Orji Uzor Kalu ne a kan gaba wajen neman kujerar Ahmad Lawan
  • Yadda jam’iyyar APC tayi kason kujerun zai yi tasiri wajen wadanda za su samu mukamai a majalisa ta 1-

Abuja - Bayanan da aka samu daga wajen hukumar INEC ya tabbatar da cewa an samu sakamakon zaben ‘yan majalisar dattawa 98 a cikin 109.

Vanguard ta ce jam’iyyu bakwai su ke da wakilci a majalisar amma a duka majalisun tarayyar, jam’iyyar APC ta ke da rinjaye da kujeru 57 da kuma 162.

Hakan yana nufin shugabancin majalisa ya na hannun jam’iyyar APC, kuma ta kai an fara shirye-shiryen wadanda za su rike mukamai a wannan karo.

Kara karanta wannan

Ku taimake ni: Gwamnan PDP ya yi murya kasa-kasa, ya roki mata alfarma a zaben ranar Asabar

Ba da dadewa ba ake sa ran jam’iyya mai-ci za ta fitar da yadda za a kasa kujerun majalisa. Za a ware kujeru zuwa wani yanki domin ayi adalci.

Arewa maso yamma da Kudu maso gabas

Tun da Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shetima sun fito daga Kudu maso yamma da Arewa maso gabas ne, za a raba sauran mukaman ga wasu bangarori.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton ya ce shugaban masu tsawatarwa a majalisar dattawa a yanzu haka, yana cikin wadanda suka kwallafa rai a kan kujerar shugaban majalisar.

Majalisa
Shugaban Majalisar Dattawa Hoto: Ahmad Lawan
Asali: Twitter

Sannan akwai Sanata Goodwill Akpabio daga Kudu maso kudu da ya fara neman kujerar. Tsohon Gwamnan ya rike Ministan Neja-Delta a mulkin APC.

A majalisar wakilai, Hon. Aliyu Betara wanda ya lashe zabe a karo na biyar yana harin kujerar. Sai dai wasu na ganin mukamin na Arewa maso yamma ne.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Tona Wadanda Suka Fatattaki Peter Obi Daga Jam’iyyar PDP Daf da Zabe

Idan daga Arewa maso yamma za a samu shugaban majalisar wakilai, irinsu Hon. Alhassan Ado Doguwa sun ci buri, sai dai yanzu yana tsare a gidan yari.

Wasu sun soma yin kamfe

Wata majiya ta shaidawa Punch cewa akwai wani tsohon Gwamna daga Kudu maso gabas da ya fara tallata manufarsa ta zama shugaban majalisar dattawa.

Sannan irinsu Adam Oshiomhole wanda wannan ne karon farko da suka shigo majalisa, su na sa ran samun mukami mai tsoka da zarar an rantsar da su.

Shekarau zai zama Sanata?

Duk da ya bar Jam’iyya watanni 9 da suka wuce, rahoto ya zo cewa INEC ta ce Ibrahim Shekarau ne ya lashe zaben Sanatan Kano ta tsakiya a NNPP.

Sanata Ibrahim Shekarau aka sanar a matsayin wanda ya yi galaba. Amma NNPP ta ce Rufa’i Sani Hanga ne asalin ‘Dan takaranta da ya samu kuri’u 456, 000.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnoni: Buhari Ya Bada Hakuri Kan Canjin Kudi, Ya Bayyana ‘Yan Takaransa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng