“Kayan Da Bai Da Ko Kyau”: Bidiyon Leshin N4.5m Ya Haddasa Cece-Kuce

“Kayan Da Bai Da Ko Kyau”: Bidiyon Leshin N4.5m Ya Haddasa Cece-Kuce

  • Wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya ya nuno wata matashiya tana tallata leshi da kudinsa ya kai miliyoyi
  • A cewar bidiyon, farashin leshin shine naira miliyan 4.5 kan kowani yadi 5
  • Masu amfani da soshiyal midiya da dama da suka ga bidiyon sun tofa albarkacin bakunansu

Masu amfani da soshiyal midiya sun yamutsa gashin baki bayan cin karo da wani bidiyo da ya yadu na wata dilalliyar kaya tana tallata leshi masu rai da motsi.

Idan aka zo kan maganar tsadaddun leshi na kece raini, shakka babu manyan mata kan saki bakin aljihu don kerewa sa’a.

Matashiya na tallata zanin leshi
“Kayan Da Bai Da Ko Kyau”: Bidiyon Leshin N4.5m Ya Haddasa Cece-Kuce Hoto: @moshade_fabrics
Asali: Instagram

Wani bidiyon dillaliyar kaya, @moshade_fabrics ya bayyana a soshiyal midiya inda aka gano ta tana tallata wani dankareren leshi.

A bidiyon, an jiyo ta tana cewa farashin leshin ga masu siyan daddaya shine naira miliyan 4.5 kan kowani yadi 5.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Wasu Tsageru Sun Yanka Jagoran APC Har Lahira Bayan Tinubu Ya Ci Zabe

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani

inyanga_crafts:

"Ba wai batun farashin bane kawai koda a kan 4500 kowani yadi ne ba zan siya ba saboda bai da kyau ko kuma in ba haka ba kamararki ne."

brown_signature:

"Yadin da bai da kyau kamar leshi mai araha."

pearlbeni:

"Yadi ne daga aljannah."

_kasham__:

"Idan na siya wannan yadin kullun zan dunga sakawa, zan yi amfani da yadi 5 din wajen dinka wando, doguwar riga, siketi, zani idan ba a samu dankwali ba akwai matsala fa."

lolashode:

"Martaba suke siyarwa ba kayan ba."

stitchesbylami:

"Kudi da zan yi amfani da shi wajen siyan fili na yi tubali ma."

ceemirabelscynosure:

"Zan siya leshi mai kyau...na yi amfani da sauran kudin wajen samar da madogara ga sauran iyalai. Abubuwa da yawa da mutum zai yi da kudin yanzu a Najeriya."

Kara karanta wannan

Sakamakon Zaben 2023: A Karshe Babban Sarkin Yarbawa Ya Magantu Kan Soke Zabe Da Obasanjo Ya Ce A Yi

pre_k_cute:

"Kasuwanci wani kacokan ne wannan leshin yadi 5 faaaaa. ha akwai Allah ❤️ zai kai kanmu mu dukka."

Bidiyon yadda matashi ya dinke N100 da keken dinki ya ba da mamaki

A wani labarin kuma, wani matashi ya bar mutane baki bude bayan bidiyonsa ya yadu a soshiyal midiya inda aka gano shi yana dinke takardar N100 a kan keken dinki sai kace ya samu zani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel