Naziru sarkin waka ya cire mun kebura 99 a jikina – Fati Slow

Naziru sarkin waka ya cire mun kebura 99 a jikina – Fati Slow

  • Fati Slow Motion ta yi tsokaci a kan yadda aka kawo karshen takkadamar da ya faru kwanakin baya a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood
  • Tsohuwar jarumar fim din ta bayyana cewa sai da ta kwana bata ritsa ba sakamakon kalaman da ta yi a kan Naziru sarkin waka a lokacin takkadamar
  • Ta kuma bayyana cewa sarkin waka ya cire mata kebura 99 a jikinta, inda ta ce ba za ta taba mantawa da shi ba a rayuwarta

Tsohuwar jarumar Kannywood, Fati Usman wacce aka fi sani da Fati Slow Motion ta magantu a kan yadda aka kai karshen takkadama da ya faru a masana'antar ta shirya fina-finan Hausa kwanakin baya a hirarta da BBC Hausa.

Jarumar ta bayyana cewa masana'antar fim ta yi masu uwa ta yi masu uba shiyasa ta fito ta yi magana tun farko.

Kara karanta wannan

Bidiyon katafaren gidan bene na alfarma da jaruma Rukayya Dawayya ta gina wa kan ta

Fati ta bayyana cewa komai ya zo karshe ne bayan Naziru sarkin waka ya tsamo ta daga yanayi na kebura (talauci) da take ciki domin a cewarta, sai da ya cire mata kebura 99 daga jikinta.

Naziru sarkin waka ya cire mun kebura 99 a jikina – Fati Slow
Fati Slow ta ce ba za ta taba mantawa da Naziru ba a rayuwarta Hoto: BBC Hausa
Asali: UGC

Ta kuma yi kira ga al’ummar Annabi da su dunga taimakawa mutane, cewa ta hakan ne lamura za su daidaita a wannan yanayi da ake ciki.

A cikin shirin ‘Daga bakin mai ita’ na sashin Hausa na BBC, an tambayi tsohuwar jarumar game da yadda aka yi aka kawo karshen takkadamar da ya faru sakamakon cece-kuce da aka yi kwanakin baya, sai Fati ta ce:

“Dalili ka ga ita wannan masana’anta ta industiri mu babu abun da za mu ce da ita. Ta yi mana uwa, ta yi mana uba. Don haka da wannan abun ya zo ya faru na sarkin waka wato Naziru na fito na yi maganganu, har na fadi wasu kalma guda biyu a kanshi.

Kara karanta wannan

Bidiyon Wata 'Yar Najeriya Da Ta Gano Ashe 'Yar Aikinta Gardi Ne Bayan Wata 3, Ta Tozarta Shi

“Saboda da na zo na fadi kalmar nan guda biyu a kan Naziru sai da na kwana ban yi bacci ba, saboda na yi mai karu. Karun nan da nayi masa sai ya zamana hankalina ya tashi sai nake ta tunani, haka na kwana ina tunani saboda ina tsoron a rayuwata ta duniya, ina tsoron ranar da zan tashi a gaban Allah da ya halicceni tunda na yi furuci wanda yana da bukatar shaidu. Don haka sai na zo da Mansura Isah dani muka je wajen sarkin waka kafin ma in je wajen shi ya ce ya yafe mun.
“Kuma kamar a kalamansa da ya yi, ba karya bane mutane da yawa, ana ta karbar kebura a nan garin, ni kaina na karbi kebura. Naziru sarkin waka sai da ya cire mun kebura 99 a jikina. Yanzu dan Allah a samu al’ummar Annabi Muhammad SAW su dunga ragewa mutane kebura a jikinsu, wallahi komai zai warware. Yanzu misali, sarkin waka ya dauki kudi naira miliyan daya ya bani yace gashi Fati ki je ki ja jari. Yanzu dan Allah ta yaya za a yi in manta da wannan bawan Allah a rayuwata ta duniya.”

Kara karanta wannan

An kore shi daga aiki bayan matarsa ta zagi shugabansa, ta kwashe kudadensa ta tsere

Bidiyon Fati Slow yayin da take ba Naziru sarkin waka hakuri bayan ta kunshe miliyan N1 da ya bata

A baya mun ji cewa Fati Slow ta yi sulhu da Naziru M Ahmad wato Sarkin Waka bayan sabanin da ya gibta a tsakaninsu.

Tun farko dai jarumar ta fito a shafin Instagram inda ta saki wasu bidiyo da dama tana sukar Sarkin wakar kan furucin da ya yi na cewa ana lalata da wasu mata kafin a saka su a fim. Harma jarumar ta kalubalance shi da ya rantse cewa shima baya aikata hakan.

Ana haka sai Naziru ya fito ya yi martani inda ya nuna cewa bai ji zafin abun da Fati Slow ta yi ba, hasalima ya ce ya lura tana bukatar taimako saboda haka ya yi mata kyautar naira miliyan daya domin ta ja jari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel