An Yi Rashin Jarumin Fina Finai Kwanaki da Rasa Daso a Duniyar Wasan Kwaikwayo

An Yi Rashin Jarumin Fina Finai Kwanaki da Rasa Daso a Duniyar Wasan Kwaikwayo

  • Masana'antar shirya fina-finai ta Nollywood ta sake tafka babban rashi bayan mutuwar wani shahararren jarumi
  • A yammacin jiya Talata 23 ga watan Afrilu ne aka sanar da mutuwar jarumi Zulu Adigwe wanda ya ta da hankula
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai shirya fina-finai a masana'antar, Stanley Nwoke a shafinsa a Instagram

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - An sake tafka babban rashi bayan fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Zulu Adigwe ya riga mu gidan gaskiya.

An sanar da rasuwar marigayin a yammacin jiya Talata 23 ga watan Afrilun wannan shekara.

Fitaccen jarumin fina-finai ya kwanta dama a Najeriya
Jarumin fina-finan Nollywood, Zulu Adigwe ya rasu. Hoto: @zuluadigwe.
Asali: Instagram

Yaushe aka sanar da mutuwar jarumin fina-finan?

Kara karanta wannan

An shiga jimami yayin da tsohon Sarki a Yobe ya rasu a Saudiyya a shekaru 82

Mai shirya fina-finai a Nollywood, Stanley Nwoke ya tabbatar da haka a shafinsa na Instagram ba da dadewa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Stanley ya bayyana cewa har zuwa lokacin sanar da mutuwar marigayin ba a gano musabbabin mutuwar tasa ba.

"Ina mai bakin cikin sanar da ku cewa fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Zulu Adigwe ya rasu."
"Har yanzu ba a fayyace musabbabin mutuwar jarumin ba, Allah ya masa rahama."

Lokacin da ya ke raye, Adigwe ya yi shura a fina-finai kamar su 'Living in Bondage' da 'Breaking Free' da sauransu.

- Stanley Nwoke

Martanin 'yan Najeriya kan mutuwar jarumin

Bracha_blessing:

"Abin takaici dukkan manyan jarumai suna tafiya, kusan sun kusa karewa."

Adanne:

"Na gaji da rubuta da RIP kan jaruman Nollywood, don Allah ku daina mutuwa haka."

sweet_awilo:

Kara karanta wannan

Neman kudi: "Mun kashe Bafullatana domin yin tsafi", malamin tsibbu ya fallasa abokansa

"Mutane kullum sai mutuwa suke kawai saboda mun san su ne shiyasa muke ganin kamar a Nollywood ne kadai, wannan duniya ba ta mu ba ce, ka yi abin kirki kafin ka barta."

Jarumar fina-finan Kannywood, Daso ta rasu

A wani labarin, kun ji cewa Allah ya karbi rayuwar fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood, Saratu Gidado wacce aka fi sani da Daso.

Rahotanni sun tabbatar da cewa ta ce an samu labarin rasuwar marigayiyar a ranar Talata 9 ga watan Afrilun 2024.

Yan uwan marigayiyar sun tabbatar cewa ta rasu ne yayin da ta ke cikin bacci bayan kammala Sahur na watan Ramadan..

Asali: Legit.ng

Online view pixel