Bidiyon Fati Slow yayin da take ba Naziru sarkin waka hakuri bayan ta kunshe miliyan N1 da ya bata

Bidiyon Fati Slow yayin da take ba Naziru sarkin waka hakuri bayan ta kunshe miliyan N1 da ya bata

  • Tsohuwar jarumar Kannywood, Fati Usman wacce aka fi sani da Fati Slow ta ba Naziru Sarkin Waka hakuri a kan tabarar da ta yi masa a shafin soshiyal midiya
  • Fati Slow wacce ta tabbatar da cewar mawakin ya bata kyautar naira miliyan daya, ta ce dama dai rashin kudi ne ke damunta wanda kowa ya san ta
  • Rikicin nasu dai ya samo asali ne kan sharhi da shi Naziru ya yi game da batun Ladin Cima

Shahararriyar tsohuwar jarumar Kannywood, Fati Usman wacce aka fi sani da Fati Slow ta yi sulhu da Naziru M Ahmad wato Sarkin Waka bayan sabanin da ya gibta a tsakaninsu.

Tun farko dai jarumar ta fito a shafin Instagram inda ta saki wasu bidiyo da dama tana sukar Sarkin wakar kan furucin da ya yi na cewa ana lalata da wasu mata kafin a saka su a fim. Harma jarumar ta kalubalance shi da ya rantse cewa shima baya aikata hakan.

Kara karanta wannan

Ta Musamman ce: Bidiyon yadda mata ta biya wa mijinta bashin N1.3m ya bar jama'a baki bude

Bidiyon Fati Slow yayin da take ba Naziru sarkin waka hakuri bayan ta kunshe miliyan N1 da ya bata
Fati Slow ta ba Naziru sarkin waka hakuri bayan ta kunshe miliyan N1 da ya bata Hoto: fatee_slow
Asali: Instagram

Ana haka sai Naziru ya fito ya yi martani inda ya nuna cewa bai ji zafin abun da Fati Slow ta yi ba, hasalima ya ce ya lura tana bukatar taimako saboda haka ya yi mata kyautar naira miliyan daya domin ta ja jari.

Tun bayan nan ba a sake ji jarumar ta fito ta kuma caccakarsa ba, sai a yanzu ne ta fito tana bashi hakuri.

A wani bidiyo da ta wallafa a shafin nata, Fati ta ce dama chan talauci ne ke damunta amma ta nutsu yanzu.

Ta kuma tabbatar da cewar mawakin ya bata naira miliyan dayan da ya yi mata alkawari inda ta nemi yafiyarsa a kan cin mutuncin da tayi masa.

An jiyo Fati na cewa:

Kara karanta wannan

Ni 'yar Drama ce, 'yar Nanaye, ina alfahari da hakan, Maryam Booth

“Ga ni ga sarkin waka Naziru, nagode Allah ya saka da alkhairi, ya bani naira miliyan daya. Dama harkace ta kebura (talauci) kuma babu wanda bai san ta ba. Na nutsu yanzu. Komai ya wuce sarki ka yi hakuri, Wallahi na yi maka hau, kuma ka ce ka yafe mun Alhamdulillahi wallahi nagode ma Allah, wannan ma arziki ce a rayuwa ta duniya.”

Naziru sarkin waka ya yiwa Ladin Cima da Fati Slow kyautan miliyoyi naira

A baya mun ji cewa Mawakin Kannywood, Naziru Sarkin waka ya tare da yayyensa da ke masana'antar shirya fina-finan sun yi wa dattijuwar jaruma, Ladin Cima kyautar kudi naira miliyan biyu.

Naziru a cikin bidiyon da ya wallafa a shafinsa na Instagram, ya ce sun yi mata kyautar wannan kudi ne domin ta ja jari ta yadda za ta dunga samun na cin abinci. Ya kuma ce idan Allah ya barsu da rai za su dunga tallafa mata lokaci zuwa lokaci.

Kara karanta wannan

Sauki ya samu: Sabbin hotuna da bidiyon Maryam Yahaya a kasar Dubai

Hazalika ya ce an tura masa bidiyon abokiyar sana'arsa Fati Usman wacce aka fi sani da Fati Slow inda take ta raddi kan furucin da yayi a baya game da yadda ake lalata da mata a masana'antar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel