Dr Girema ta shirin Kwana Casa'in ta ja kunnen 'yan mata masu son shiga harkar fim

Dr Girema ta shirin Kwana Casa'in ta ja kunnen 'yan mata masu son shiga harkar fim

  • Jaruma Saratu Abubakar Zazzau wacce akaa fi sani da Dakta Girema a shirin Kwana Casa'in, ta shawarci 'yan mata masu son shiga harkar fim
  • A hirar da aka yi da jarumar, ta ce duk mace da ke son shiga masana'antar, ta hakura kada ta shiga, idan kuma dole ne, ta samu jagorancin iyaye
  • Ta yi magana kan batun cewa matan masana'antar basu zaman aure inda tace ba haka bane, babu macen da za ta yi aure ta so ta fito

Jaruma Saratu Abubakar Zazzau wacce aka fi sani da Dakta Girema a shirin Kwana Casa'in mai dogon zango ta bada shawara ga mata masu sha'awar shiga masana'antar Kannywood da cewa wacce bata shigo ba kada ta shigo.

Idan kuma za ta shigo ta samu jagoranci na gari da ita a sa ta hannu na gari yayin shiga masana'antar, kamar yadda Daily Trust Aminiya ta zanta da jarumar.

Kara karanta wannan

Bidiyon katafaren gidan bene na alfarma da jaruma Rukayya Dawayya ta gina wa kan ta

Dr Girema ta shirin Kwana Casa'in ta ja kunnen 'yan mata masu son shiga harkar fim
Dr Girema ta shirin Kwana Casa'in ta ja kunnen 'yan mata masu son shiga harkar fim. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A cikin hirar, an mata tambayoyi da dama da suka shafi sana'ar ta da rayuwa har aka tabo mata batun matan Kannywood basa zaman aure inda ta bayyana cewa duk duniya ana sakin aure.

Kawai na Kannywood ne ya fito amma babu macen da ta ke so tayi aure a sake ta musamman su 'yan fim da Allah ya rufa musu asiri suke auren masu kudi, mutunci da tarbiya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamanta:

"Yam mata masu son harkar fim ko masu son shiga harkar fim in basu shigo ba kar su shigo. Idan kuma dole sai sun shigo, iyayensu su yi musu rakiya. Su tabbatar da sun damka su a hannu nagari wanda zai dinga kula da shige da ficensu a lokeshin da tarbiyyarsu."

Batun lalata da matan fim: Nafisa Abdullahi ta saki martani ga Sarkin waka

Kara karanta wannan

Jaruma Hafsat Idris ta magantu a kan batun aurenta, hoton matashin mijinta ya bayyana

A wani labari na daban, kamar yadda Legit.ng ta gano, batun da yafi yi wa 'yan Kannywood zafi a maganar sarkin waka shi ne batun lalata da mata kafin a saka su a fim inda matan Kannywood ke ta fitowa suna musanta waccan maganar da yayi.

Jaruma Nafisa Abdullahi ta rubuta budaddiyar wasika cikin harshen turanci a shafinta na Instagram kuma ta kara da bayani a kasan wasikar da harshen Hausa inda ta bayyana cewa babban zargi ya fitar tunda ta na cikin matan masana'antar.

Jarumar ta yi kira ga sarkin wakan idan ya na da matsala da wani ne, ya bayyana sunansa su yi ta kare ba wai ya bata masana'antar ba baki daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel