Hotunan kafin aure na Furodusa Maishadda da jaruma Aishatul Humaira sun bayyana

Hotunan kafin aure na Furodusa Maishadda da jaruma Aishatul Humaira sun bayyana

  • Kyawawan hotunan kafin aure na Furodusa Abba Bashir Maishadda da jaruma Aisha Ahmad Idris wacce aka fi sani da Aishatul Humaira sun bayyana
  • Tun farko dai, an fara rade-radin cewa Furodusan zai angwance a watan Maris, sai dai kuma ba a bayyana wacece amaryar ba
  • Da kanshi ya je shafinsa na Instagram inda ya sanar da cewa zai yi wuff da jakadiyar gishirin Dangote tare da saka hotunansu na kafin aure

A safiyar Alhamis ne aka wayi gari da sabbin kyawawan hotunan kafin aure na furodusa a masana'antar Kannywood, Abba Bashir Maishadda da jaruma Aishatul Humaira.

Tun farko dai, shafin Labaran Kannywood a Twitter a kwanaki biyu da suka gabata sun bayyana cewa furodusan zai angwance a cikin watan Maris mai kamawa, sai dai ba a san wacece amaryar ba.

Kara karanta wannan

Ayiriri: Jaruma Aisha Aliyu Tsamiya za ta shiga daga ciki a ranar Juma'a mai zuwa

Hotunan kafin aure na Furodusa Maishadda da jaruma Aishatul Humaira sun bayyana
Hotunan kafin aure na Furodusa Maishadda da jaruma Aishatul Humaira sun bayyana. Hoto daga @realabmaishadda
Asali: Instagram

Kwatsam babu zato balle tsammani, sai ga furodusan da kansa ya wallafa hotunansa tare da jaruma Aishatul Humaira inda ya bayyana cewa aurenta zai yi.

Kamar yadda wallafar tace: "Zan yi wuff da gishiri ambassador."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan wallafar da yayi, jaruma Aishatul Humaira ta sake wallafa hotunan a shafinta na Instagram inda ta hada da alamar soyayya.

Sai dai ko bayan bayyanar hotunan, babu takamaiman lokacin auren da Furodusa Abba Bashir Maishadda ya sanar ko kuma amarya Aishatul Humaira.

Ayiriri: Jaruma Aisha Aliyu Tsamiya za ta shiga daga ciki a ranar Juma'a mai zuwa

A wani labari na daban, labari mai dadi da ke bayyana a masana'antar Kannywood shi ne batun auren fitacciyar jaruma Aisha Aliyu Tsamiya. Majiyoyi masu yawa sun tabbatar da cewa za a daura auren a ranar Juma'a mai zuwa.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kashe Ɗalibin BUK, Sule, Da Ya Kammala Digiri Da 1st Class

Shafin Labaran Kannywood na Twitter ya fara wallafa labarin amma sai dai sun sanar da cewa jita-jita ce babu tabbaci. A wallafar da shafin yayi, ya ce:

"Mun samu jita-jitar cewa a ranar Juma'ar nan mai zuwa jaruma Aisha Tsamiya za ta amarce... Kuma angon nata babban mutum ne."

Duk da bahaushe na cewa, in ka ji gangami, toh tabbas akwai labari. Hakan yasa Legit.ng ta garzaya domin nemo muku bayani mai gamsarwa.

A matakin farko, Legit.ng ta fada kafar sada zumuntar zamani ta Instagram inda ta fara bin shafukan abokan sana'arta. A karon farko, mun ci karo da wallafar jarumi Ali Nuhu inda ya saka hoton jarumar tare da yi mata fatan alheri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel