Bidiyoyin jaruman Kannywood mata da Hafsat Idris inda suke girgijewa a sunan jikar ta

Bidiyoyin jaruman Kannywood mata da Hafsat Idris inda suke girgijewa a sunan jikar ta

  • Jaruman Kannywood mata kwan su da kwarkwatarsu sun halarci shagalin bikin sunan jikar jaruma Hafsat Idris
  • A cikin jaruman da suka yi wa Hafsat Idris kara akwai Mansura Isah, Rukayya Dawayya, Samira Ahmad, Ainau Ade da sauransu
  • An ga yadda jaruman suka girgije tare da cashewa a sunan jikar Hafsat Idris wacce aka yi wa jarumar takwara da ita

Kano - Jarumar Kannywood ta shirya kasaitacciyar liyafar shagalin bikin suna, bayan diyar ta da ta aurar a shekarar da ta gabata ta sunkota mata jika wacce aka yi mata takwara da ita.

Jaruman Kannywood mata ba a bar su a baya ba, sun halarci sunan kwan su da kwarkwatarsu domin nuna kara da murna ga fitacciyar jarumar.

Kara karanta wannan

Gaskiya 6 da ya kamata ku sani game da Jaruma Sadiya Haruna da Kotu ta ɗaure

Bidiyoyin jaruman Kannywood mata da Hafsat Idris inda suke girgijewa a sunan jikar ta
Bidiyoyin jaruman Kannywood mata da Hafsat Idris inda suke girgijewa a sunan jikar ta. Hoto daga @official_hafsatidris
Asali: Instagram

A bidiyoyin da Legit.ng ta tattaro a shafin Instagram na jaruma Hafsat Idris, an ga yadda jaruman mata suka dinga kwasar rawa cike da murna tare da nishadi yayin da suka halarci sunan.

Daga cikin fitattun jarumai mata da Legit.ng ta hango a bidiyoyin liyafar akwai Aina'u Ade, Samira Ahmad Rukayya Dawayya, Mansura Isah da sauransu.

Daukar hoto da gawar mahaifinta ya jawo cece-kuce - Jaruma Hafsat Idris

A wani labari na daban, Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, Allah ya yi wa mahaifin fitacciyar jarumar Kannywood, Hafsat Idris, rasuwa.

Kamar yadda hoton da jarumar ta wallafa a shafinta na Instagramya bayyana, akwai alamu dake nuna dakin asibiti, akwai yuwuwar mahaifin nata ya rasu ne a asibiti bayan jinya.

Kara karanta wannan

Nasara: Yan bindiga sun kwashi kashin su a hannu yayin da suka kai hari Ofishin yan sandan Kogi

Jaruma Hafsat Idris na daya daga cikin jarumai mata na masana'antar da suke jan zarensu a cikin wannan karnin.

Ta wallafa hotonta rike da gawar mahaifinta a shafinta na Instagram inda ta yi rubutu kamar haka: "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, Allah yayi wa mahaifina rasuwa. Allah yaji kanshi da rahama".

A hoton da jarumar ta wallafa rike da gawar ta mahaifinta, ya bayyana idonunta sun yi jawur, alama da ke nuna jarumar ta sha kuka. Tuni dai abokan aikinta da masoyanta suka dinga tururuwa wajen mika ta'aziiyarsu ga fitacciyar jarumar.

Sai dai kash! Wasu ma'abota amfani da kafafen sada zumuntar zamanin sun caccaketa bayan yi mata ta'aziyyar. Suna ganin rashin dacewar daukar hoto da gawar mahaifin nata. Wannan ba komai yake nunawa ba face rashin da''a tare da girmamawa ga mahaifin nata da ya kwanta dama, kamar yadda suka ce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel