Daukar hoto da gawar mahaifinta ya jawo cece-kuce - Jaruma Hafsat Idris

Daukar hoto da gawar mahaifinta ya jawo cece-kuce - Jaruma Hafsat Idris

Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, Allah ya yi wa mahaifin fitacciyar jarumar Kannywood, Hafsat Idris, rasuwa. Kamar yadda hoton da jarumar ta wallafa a shafinta na Instagramya bayyana, akwai alamu dake nuna dakin asibiti, akwai yuwuwar mahaifin nata ya rasu ne a asibiti bayan jinya.

Jaruma Hafsat Idris na daya daga cikin jarumai mata na masana'antar da suke jan zarensu a cikin wannan karnin.

Ta wallafa hotonta rike da gawar mahaifinta a shafinta na Instagram inda ta yi rubutu kamar haka: "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, Allah yayi wa mahaifina rasuwa. Allah yaji kanshi da rahama".

DUBA WANNAN: A matse nake in yi aure - Jaruma Saima Muhammad

A hoton da jarumar ta wallafa rike da gawar ta mahaifinta, ya bayyana idonunta sun yi jawur, alama da ke nuna jarumar ta sha kuka.

Tuni dai abokan aikinta da masoyanta suka dinga tururuwa wajen mika ta'aziiyarsu ga fitacciyar jarumar.

Sai dai kash! Wasu ma'abota amfani da kafafen sada zumuntar zamanin sun caccaketa bayan yi mata ta'aziyyar. Suna ganin rashin dacewar daukar hoto da gawar mahaifin nata. Wannan ba komai yake nunawa ba face rashin da''a tare da girmamawa ga mahaifin nata da ya kwanta dama, kamar yadda suka ce.

Muna mishi fatan rahamar Allah tare da kwanciya wacce zata zama hutu a gareshi. Ubangiji ya ba iyalansa hakurin jure rashinsa. Ameen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel