Na yi sa'ar samunki: Ali Nuhu ya yada kyawawan hotunan bikin tuna ranar haihuwar 'yarsa

Na yi sa'ar samunki: Ali Nuhu ya yada kyawawan hotunan bikin tuna ranar haihuwar 'yarsa

  • Shahararren jarumin Kannywood, Ali Nuhu ya bayyana a bikin taya diyarsa, Fatima murna yayin da ta kara shekara
  • Jarumin ya yiwa Fatima kalamai masu dadi yayin da yake magana cikin jin dadi game da yadda ya samu sa'ar samun diya kamarta
  • Ali Nuhu ya bayyana soyayyar uba ga diya tare da yiwa Fatima fatan alheri kuma masoyansa sun taya ta murna

Fitaccen jarumin fina-finan Kannywood, Ali Nuhu ya yiwa diyar sa Fatima da ke murnar zagayowar ranar haihuwarta kalamai masu dadi.

Jarumin ya bayyana a shafinsa na Instagram, inda ya yada wani kyakkyawan hotonsa da ‘yarsa tare da Fatima tare da bayyana irin sa’ar da ya samu da samun 'ya kamar ta.

Ali Nuhu da 'yarsa
Na yi sa'ar samunki: Ali Nuhu ya yada kyawawan hotunan bikin tuna ranar haihuwar 'yarsa | Hoto: @realalinuhu
Asali: Instagram

Ali Nuhu ya yi magana cikin jin dadi game da bajintar Fatima kuma ya bayyana cewa ya yi sa’a da samun ta a matsayin ‘ya:

Kara karanta wannan

Hular Tinubu ta yi daraja a kasuwar intanet, 'yan Najeriya sun yi tururuwa domin saye

"Yarinya mai 'yan hali da soyawa irinki da kyar a samu, kuma nayi sa'a da samun diya mace mai kyau irinki. Ina taya ki murnar zagayowar ranar haihuwarki 'ya ta @fatimaalinuhu Allah ya albarkace ki, ya kare ki Ameen."

Taya murnar ranar haihuwa

Masoyan Ali Nuhu da sauran manyan jarumai ne suka hadu wajen taya diyarasa murnar zagayowar ranar haihuwarta tare da yi mata addu'o'in fatan alheri.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin 'yan soshiyal midiya, karanta a kasa:

Uzee_usman:

"Happiest birthday FATI yar baba."

Oputeval:

"Wowwww. Happy birthday dear Fatima. Allah ya miki albarka a yau da ma kullum."

Firdausi.bello.355:

"Happiest Birthday Fatiti..Allah rayaki musha biki."

Sanimaikatanga_hoton:

"Ina taya ki murnar zagayowar ranar haihuwa da ci gaban rayuwa."

Kara karanta wannan

Iyalin mamaci sun mayarwa Gwamnati kudin Albashin shekara 11 da ya karba ba ya zuwa aiki

Abduljagaba:

"Ranku ya dade sarki da diyarka."

Yunumustapha:

"Karin shekaru da wadata mafi kyau daga Allah Ta'ala."

Farhanmuhammad3455:

"Tsawon rayuwa da wadata 'yar uwa."

A wani labarin, yayin da jama'a ke ci gaba da hasashen yadda babban zaben kasar na 2023 zai kasance, an gano wani fostan yakin neman zabe na shahararren mawakin nan na masana'antar shirya fina-finai na Kannywood, Ali Isa Jita.

Fostan wanda abokiyar sana'arsa Rahama Sadau ta wallafa a shafinta na Instagram, ya nuna cewa mawakin zai fito takarar kujerar gwamnan jihar Kano ne a zaben na 2023.

Sai dai kuma babu suna ko tambarin wata jam'iyyar siyasa a cikin hoton wanda ke dauke da rubutu kamar haka 'hangen nesa, sha'awa, aiki Jita 2023, Ali Isa Jita don neman gwamna, jihar Kano, Insha Allah'.

Read more: https://hausa.legit.ng/kannywood/1451316-fostan-ali-jita-na-takarar-kujerar-gwamnan-kano-ya-fara-yawo-a-shafin-soshiyal-midiya/

Asali: Legit.ng

Online view pixel