Kannywood: Dalilin da yasa muka maida fina-finan Hausa kan Youtube, Sarki Ali Nuhu

Kannywood: Dalilin da yasa muka maida fina-finan Hausa kan Youtube, Sarki Ali Nuhu

Shahararren jarumi a masana'antar shirya fina-finan Hausa Kannywood, Ali Nuhu, ya bayyana cewa suna amfani da zamani wajen tafiyar za harkokinsu.

Ali Nuhu, wanda aka fi sani da Sarki Ali a Kannywood, ya ƙara da cewa sun koma amfani da manhajar Youtube ne sabida zamani ya zo da haka kuma ta nan ne zaka samu kudinka a dunƙule.

A wata fira da BBC Hausa, Sarki Ali yace zuwan Youtube ya kassara jarin wasu, yayin da wasu kuma suka samu cigaba musamman masu kirkirar shiri da kansu.

Jaruman Kannywood
Kannywood: Dalilin da yasa muka maida fina-finan Hausa kan Youtube, Sarki Ali Nuhu Hoto: RealAliNuhu
Asali: Instagram

Sarki Ali yace:

"Masana'antar Kannywood ta na tafiya da zamani, a duk lokacin da zamani ya kawo wani sabon abu, masana'antar na juya wa zuwa wannan abun."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Da duminsa: NCAA ta garkame babban ofishin Glo na Abuja kan bashin N4.5bn

"A yanzu mutane sun fi son su shiga manhajar Youtube su kalli bidiyo, dan haka muka koma saka musu shirye-shiryen mu a kan manhajar."
"Wannan cigaba ya kassara jarin wasu a Kannywood, wasu ma sun bar masana'antar saboda suna ganin ba za su iya bin wannan cigaban da aka samu ba."

Waye Ali Nuhu?

Sarki Ali na ɗaya daga cikin fitattun jarumai a Kannywood waɗan da suka jima suna fitowa a fina-finan Hausa.

Jarumin ya fito a shirye-shirye da dama kuma a halin yanzun ana ganin shine babba a Kannywood musamman a ɓangaren jarumai maza.

Daga cikin fina-finan da yake fito wa daga cikin masu dogon zango da ake cigaba da saki akwai, Izzar So, da kuma Alaqa.

Shiri mai dogon zango na Alaqa, wanda Ali Nuhu ya bada umarni, yana ɗaya daga cikin fina-finai dake jan hankalin masu bibiyar Kannywood.

A wani labarin kuma Batun Jaruma Rahama Sadau da wasu sabbin muhimman abubuwa 4 da suka faru a Kannywood

Kara karanta wannan

El-Rufai ya tura sako ga 'yan Kaduna, ya ce su gaggauta cika shirin tallafin Korona

A wannan makon an samu wasu muhimman abubuwa guda 5 masu muhimmanci da suka faru a Kannywood.

Daga cininsu shine batun raɗin sunan jaririyar da aka haifa wa Adam Zamgo, da kuma abinda ya shafi Rahama Sadau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel