Mai yankan kauna: Rasuwar angon Disamba ta tada hankulan ma'abota Facebook

Mai yankan kauna: Rasuwar angon Disamba ta tada hankulan ma'abota Facebook

  • Hankulan jama'a sun tashi a Facebook yayin da hawaye ya kwaranya sakamakon rasuwar matashi Sani Ruba
  • Matashin dan asalin jihar Jigawa ya shirya tsaf domin angwancewa da masoyiyarsa Rafeeah Zirkarnain a ranar 11 ga watan Disamba
  • Bayanai sun nuna cewa, mutuwa ta yi wa masoyan biyu yankan kauna ne sakamakon hatsarin da Sani Ruba ya tafka a hanyar Numan zuwa Gombe

Jama'a masu tarin yawa sun kadu tare da shiga matukar tashin hankali a kafar sada zumuntar Facebook sakamakon rasuwar matashi Sani Ruba.

Duk da kowanne mai rai mamaci ne kuma rashi ya saba taba mutane, rashin Sani Ruba ya gigita jama'a ne ganin ranar 11 ga watan Disamba mai zuwa zai angwance.

Allahu Akbar: Rasuwar angon Disamba ta tada hankulan ma'abota Facebook
Allahu Akbar: Rasuwar angon Disamba ta tada hankulan ma'abota Facebook. Hoto daga aminiya.dailytrust.com
Asali: UGC

Labarin mutuwar matashin mai shekaru talatin da shidan ta bazu ne bayan wacce zai aura, Rafeeah Zirkarnain ta wallafa a shafin ta na Facebook.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Allah ya yi wa mahaifin jarumi Umar Faruk Gombe rasuwa

A sanarwar ta: "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Masoyi na Sani Ruba, ashe ba za mu kasance mata da mijin ba a ranar 11 ga watan Disamba... Tun jiya na ke jin wani iri amma na cire tunanin a rai na... Ba zan taba samun mutum irin ka ba a matsayin miji."

Tabbas wannan wallafar ta budurwa Rafeeah ta gigita mutane.

An gano cewa matashin dan asalin garin Ruba da ke jihar Jigawa ya rasu ne sakamakon hatsarin mota da ya ritsa da shi a titin Numan zuwa Gombe.

Mazaunin jihar Filaton wanda ya rasu a ranar Alhamis ya yi karatu a sashen koyar da aikin jarida na jami'ar Bayero da ke Kano.

Sabon farmakin da 'yan fashin daji suka kai Sokoto ya lamushe rayuka 14

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda iyayen matashi suka nuna farin ciki mara misali yayin da ya duba sakamakon jarrabawar zama lauya

A wani labari na daban, a kalla mutane 14 ne su ka rasa rayukansu yayin da ‘yan bindiga suka kai farmaki wasu garuruwa da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.

An kai farmakin ne bayan sa’o’i kadan da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara tura wasu sojoji zuwa jihar don kawo gyara akan matsalar tsaro, Daily Trust ta wallafa.

Wani mazaunin Sabon Birni, wanda ya tabbatar da farmakin ya ce ‘yan bindigan sun afka wasu kauyuka da ke Unguwan Lalle, a ranar Talata da dare.

A cewarsa, sun halaka wani Abdullahi Usman a Unguwan Lalle, sannan sun halaka mutane 9 a kauyen Tsangerawa da wasu 4 a Tamindawa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel