Trump Ya Yi wa Fafaroma Leo Wankin Babban Bargo bayan Masa Nasiha kan Iran
- Yayin da aka dakatar da yakin Iran, Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya kaddamar da kakkausar suka kan Fafaroma Leo XIV
- A wani sako da ya fitar, Trump ya zargi Fafaroma da rashin sanin me duniya ta ke ciki, inda ya nuna cewa Leo ya ci albarkacin Amurka
- Fafaroma Leo ya kasance daga cikin masu caccakar salon Trump na kaddamar da yake-yake a duniya, lamarin da ke shafar kasashe
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Shugaban Amurka Donald Trump ya yi kakkausar suka ga Fafaroma Leo XIV a daren Lahadi, yana cewa bai yi imanin cewa shugaban cocin Katolika ɗan Amurka yana yin aiki mai kyau ba.
A sukar da ya yi, Trump ya sanar da cewa Fafaroma Leo mutum ne mai sassauci sosai, sannan ya ce ya kamata ya daina biye wa masu adawa da shi.

Source: Getty Images
The Guardian ta wallafa cewa Trump ya soki Fafaroma ne yayin da yake dawowa Washington daga jihar Florida a daren Lahadi.
Trump ya caccaki Fafaroma Leo
Trump ya yi amfani da wani dogon rubutu domin sukar Fafaroma, sannan ya ci gaba da hakan a yayin da yake magana da ‘yan jarida a filin jirgin sama.
“Ba na son Paparoma Leo,”
In ji shi.
Rahotanni sun nuna cewa kalaman Trump sun biyo bayan furucin da Fafaroman ya yi a karshen mako kan yakin Amurka da Isra’ila da Iran.
Trump ya ce:
“Fafaroma Leo yana da rauni a kan harkokin yaki da aikata laifuffuka, kuma ba shi da kwarewa a harkokin kasashen waje,”
Ya kara da cewa:
“Ba na son Paparoma da ke ganin ya dace Iran ta mallaki makamin nukiliya.”

Source: Getty Images
Karin sukar Trump ga Fafaroma
Kafin tsagaita wuta, lokacin da Trump ya yi barazanar kai hare-hare kan tashoshin wutar lantarki da sauran muhimman abubuwan more rayuwa a Iran, Fafaroman ya bayyana irin wadannan kalamai a matsayin:
“Abin da ba za a amince da shi ba.”
A cikin sakonsa na daren Lahadi, Trump ya soki Fafaroma kan batun Iran da Venezuela.
CNN ta rahoto Trump ya rubuta cewa:
“Ba na son Fafaroma da ke ganin ba daidai ba ne Amurka ta kai hari Venezuela,”
Ya kara da cewa:
“Ba na son Fafaroma da ke sukar Shugaban Amurka saboda ina yin abin da aka zabe ni in yi da rinjayen kuri’u.”
Trump ya nemi Fafaroma ya yi gyara
Shugaba Trump ya kuma yi ikirarin cewa Fafaroman ya samu mukaminsa ne saboda shi ɗan Amurka ne, yana cewa:
“Da ban kasance a Fadar White House ba, da Leo bai kasance a Vatican ba.”
Ya bukaci Paparoman da ya “gyara halinsa,” ya yi amfani da hankali, ya daina bin 'yan adawa masu tsattsauran ra’ayi, kuma ya mayar da hankali kan zama Fafaroma nagari ba dan siyasa ba.
An nemi a gwada lafiyar Trump
A wani labarin, mun kawo muku cewa an fara kira game da neman gwajin lafiyar Shugaban Amurka, Donald Trump saboda wasu dalilai.
Wani dan majalisar Amurka ya rubuta takarda ga fadar White House cewa ya kamata a yi wa shugaba Trump gwajin kwakwalwa.
'Dan majalisar ya jero wasu maganganu da Trump ya yi bayan fara yakin Iran da ya ce sun nuna alamun shugaban kasar yana da matsala.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


