Hormuz: Iran Ta Maida Martani kai Tsaye ga Kawayen Amurka bayan Barazanar Trump

Hormuz: Iran Ta Maida Martani kai Tsaye ga Kawayen Amurka bayan Barazanar Trump

  • Kasar Iran ta yi martani ga kasashe a duniya bayan barazanar Amurka game da rufe mashigar Hormuz da aka yi
  • Iran ta ce mashigan Hormuz a bude yake ga jiragen ruwa, sai dai wadanda ke da alaka da abokan gabanta, yayin da rikici ke kara tsananta
  • Jami’in Iran Ali Mousavi ya bayyana cewa jiragen da ba na makiya ba za su iya wucewa idan sun hada kai da Tehran wajen tsaro da aminci

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Tehran, Iran - Kasar Iran ta yi karin haske kan dambarwa da ake ya yi game da mashigar ruwa ta Hormuz.

Iran ta bayyana cewa mashigan Hormuz yana nan a bude ga dukkan jiragen ruwa, sai dai wadanda ke da alaka da makiyanta, kamar yadda rahotanni suka nuna.

Kara karanta wannan

Da gaske jiragen Iran sun farmaki ayarin motocin Trump? an samu gaskiyar zance

Iran ta yi martani bayan barazanar Trump kan mashigar Hormuz
Shugaban Amurka, Donald Trump da jagoran addini na kasar Iran, Mojtaba Khamenei Hoto: Reza B, Andrew Caballero-Reynolds.
Source: Twitter

Ali Mousavi, wakilin Iran a hukumar sufurin teku ta Majalisar Dinkin Duniya, ya ce jiragen da ba na makiya ba za su iya wucewa cikin tsari, cewar Reuters.

Hormuz: Barazanar da Trump ya yi ga Iran

Wannan na zuwa ne bayan Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi wa Iran barazana mai girma game da rufe mashigar Hormuz da ta yi.

Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi barazanar kai hari kan tashoshin wutar Iran yayin da ake ci gaba da yaki.

Harin makamai masu linzami daga Iran ya jikkata mutane da dama a kudancin Isra'ila, yayin da ake shirin kara tsananta hare-hare a mako mai zuwa.

Rikicin ya kara tsananta bayan harin Amurka da Isra’ila, inda Iran ta mayar da martani, lamarin da ya dagula harkokin mai da tattalin arzikin duniya.

Trump ya yi barazana ga Iran kan mashigar Hormuz
Shugaba Donald Trump na Amurka a birnin New York. Hoto: @RealDonaldTrump.
Source: Twitter

Matsayar Iran wurin hadin guiwa da ƙasashe

Ya kuma kara da cewa Iran za ta ci gaba da hadin gwiwa da hukumar IMO domin inganta tsaro da kare ma’aikatan teku a yankin Gulf.

Kara karanta wannan

Trump ya gaji da jira, ya ba Iran wa'adin awa 48 ko ya yi mata illa mai muni

Sai dai ya jaddada cewa hare-haren Amurka da Isra’ila ne suka haifar da matsalar da ake fuskanta yanzu a mashigan Hormuz, yana mai kira ga zaman lafiya.

Barazanar hare-hare a rikicin da ke gudana ta sanya jiragen ruwa da dama tsoron wucewa mashigin, wanda ke da muhimmanci wajen jigilar mai da iskar gas.

Mousavi ya ce diflomasiyya ce fifiko ga Iran, amma dole ne a dakatar da hare-hare gaba daya tare da gina amincewa tsakanin bangarorin da ke rikici.

Hakan bai rasa nasaba da yadda yakin ke ci gaba da jawo asarar rayuka daga dukan bangarorin da ke rikici da juna da aka fara tun karshen watan Faburairun shekarar 2026.

Shawarar kasashen Turai kan bukatar Trump

Mun ba ku labarin cewa kasashen da ke karkashin kungiyar Tarayyar Tarayya sun kunyata bukatar Shugaba Donald Trump kan batun mashigar Strait of Hormuz.

A wani taro da suka gudanar, wakilan kasashen Turai sun ce suna mamakin abin da jiragen ruwansu za su yi, wanda na Amurka suka gaza.

Yakin Amurka, Isra'ila da Iran na ci gaba da zama baranzana ga tattalin arzikin duniya sakamakon tashin farashin danyen mai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com