Da Gaske Jiragen Iran Sun Farmaki Ayarin Motocin Trump? an Samu Gaskiyar Zance

Da Gaske Jiragen Iran Sun Farmaki Ayarin Motocin Trump? an Samu Gaskiyar Zance

  • An yi ta yada wasu rahotanni wai cewa jirage marasa matuki na kasar Iran sun farmki ayarin motocin Donald Trump
  • Lamarin ya jawo muhawara amma wani bincike ya yi karin haske kan ikirarin da ake yi yayin da yaki ke ci gaba da gudana
  • Hotunan da aka yada tare da labarin an gano cewa kirkirarru ne ko an sauya su, wasu ma daga wata ziyara ce ta daban

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tehran, Iran - Wasu rahotanni sun yi ta yawo cewa cewa an kai hari kan jerin motocin shugaban Amurka, Donald Trump.

Wannan jita-jita na zuwa ne yayin da ake ci gaba da yaki tsakanin Iran da Isra'ila da ke samun goyon bayan Amurka a Gabas ta Tsakiya.

An karyata rahoton harin Iran kan Trump
agoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei da Shugaba Donald Trump. Hoto: Getty Images.
Source: Facebook

Rahoton da ake yadawa na hari kan Trump

Kara karanta wannan

Yadda rade radin mutuwar Netanyahu ke karuwa duk da bayyanar shi a bidiyo

Binciken kwa-kwaf daga Dubawa ya bayyana cewa ikirarin da ake yadawa a kafafen sada zumunta cewa babu gaskiya ko kadan.

An yada labarin cewa wasu jami’an Iran sun kai hari wanda ya haddasa mummunan hatsarin mota, inda aka ce sama da mutane 248 sun jikkata, yayin da akalla 10 suka mutu.

Labarin ya jaw muhawara a kafofin sadarwa duba da yadda yaki ya yi tsami tsakanin Iran da Isra'ila da kuma Amurka karkashin jagorancin Donald Trump.

Gaskiyar jita-jitar da ake yadawa kan Trump

Sai dai binciken ya nuna babu wata kafar yada labarai mai inganci da ta ruwaito irin wannan lamari, duk da muhimmancin Trump wanda zai sa labari ya bazu cikin gaggawa.

Haka kuma babu wata sanarwa daga gwamnatin Amurka ko hukumomin tsaro da ta tabbatar da cewa an kai hari ko cewa Trump ya shiga wani hatsarin mota.

Binciken hotunan da aka yada ya nuna cewa an kirkire su ne ta hanyar fasahar zamani ko kuma an gyara su domin yaudarar jama’a.

Ana ci gaba da kai hare-hare a yakin Isra'ila da Iran
Shugaba Donald Trump na Amurka yayin kamfe a New York. Hoto: @RealDonaldTrump.
Source: Twitter

An gano gaskiya kan hoton da ake yadawa

Kara karanta wannan

Iran: Trump zai ja baya daga yaki, ya ce sojojin Amurka za su koma gida

Wani hoto da aka danganta da harin ya fito ne daga wata ziyara da Donald Trump ya kai Qatar, inda aka nuna jerin motocin tsaro na zamani.

Saboda haka, rahoton ya kammala da cewa ikirarin cewa an kai hari kan jerin motocin Trump tare da haddasa mace-mace ba gaskiya ba ne, illa jita-jita ce kawai.

Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da kai munanan hare-hare a Gabas ta Tsakiya saboda yakin Iran da Isra'ila.

Yakin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama daga kowane bangare wanda ya jawo maganganu daga kasashen duniya.

Trump ya yi barazanar kai hari a Iran

Mun ba ku labarin cewa Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi barazanar kai hari kan tashoshin wutar Iran yayin da ake ci gaba da yaki.

Harin makamai masu linzami daga Iran ya jikkata mutane da dama a kudancin Isra'ila, yayin da ake shirin kara tsananta hare-hare a mako mai zuwa.

Rikicin ya kara tsananta bayan harin Amurka da Isra’ila, inda Iran ta mayar da martani, lamarin da ya dagula harkokin mai da tattalin arzikin duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.