Iran Ta Ƙaddamar da Harin Makami Mai Linzami kan Cibiyar Haɗa Nukiliyar Isra'ila

Iran Ta Ƙaddamar da Harin Makami Mai Linzami kan Cibiyar Haɗa Nukiliyar Isra'ila

  • Wani makami mai linzami da kasar Iran ta harba ya afka wa birnin Dimona, inda ya jikkata mutane kusan 50 ciki har da yara kanana
  • Wannan hari na zuwa ne a matsayin ramuwar gayyar harin da Amurka da Isra'ila suka kai wa ma'aikatar nukiliyar Natanz ta Iran
  • Baraguzan makamin sun haddasa gobara a gine-ginen mazauna gari kusa da babban rumbun nukiliyar Isra'ila dake hamadar Negev

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Isra'ila - Wani makami mai linzami da ƙasar Iran ta harba ya afka wa birnin Dimona dake kudancin Isra'ila.

Dumona shi ne garin da aka sani da karɓar baƙuncin babban rumbun bincike da haɗa makaman nukiliyar Isra'ila.

Makamin da Iran ta harba ya sauka a garin da rumbun nukiliyar Isra'ila yake
Bakin hayaki ya turnuke a birnin Tehran bayan harin Isra'ila a Tel Aviv. Hoto: Fatemeh Bahrami/Anadolu via Getty Images
Source: Getty Images

Iran ta farmaki cibiyar nukiliyar Isra'ila

Rundunar sojin Isra'ila ta tabbatar da cewa makamin ya yi barna kai-tsaye a kan wani gini dake cikin garin dake hamadar Negev, in ji rahoton Al-Jazeera.

Kara karanta wannan

Iran ta yi babban rashi a ranar Sallah, kakakin rundunar IRGC ya mutu a harin Isra'ila

Wannan hari na zuwa ne a matsayin ramuwar gayya bayan da dakarun hadaka na Amurka da Isra'ila suka kai harin bam kan matatar nukiliya ta Natanz dake ƙasar Iran a safiyar yau Asabar.

Birnin Dimona ya shahara a duniya saboda ginin nukiliya dake wajen birnin, wanda masana ke amanna cewa shi ne kaɗai rumbun adana makaman nukiliya a yankin Gabas Ta Tsakiya, duk da cewa Isra'ila ba ta fito fili ta tabbatar da hakan ba.

Barnar da Iran ta yi wa Isra'ila a Dimona

Hukumar agajin gaggawa ta Isra'ila, Magen David Adom, ta bayyana cewa ma'aikatanta sun yi jinyar mutane da dama a wurare daban-daban da makamin ya shafa.

Ga bayani dalla-dalla kan asarar da aka samu:

  • Akalla mutane 39 zuwa 47 ne aka kai asibitin Soroka dake Beersheba sakamakon raunuka daban-daban.
  • Wani yaro ɗan shekara 10 yana cikin wani hali mai tsanani bayan da baraguzan makamin suka fada kansa.
  • An samu wata mata 'yar shekara 40 da ta jikkata, yayin da wasu mutum 14 suka firgita sosai sakamakon fashewar.
  • Hotunan da kafafen yaɗa labaran Isra'ila suka nuna sun nuna wani gini a gari yana cin wuta, yayin da 'yan sanda suka nuna wani gini da aka fasa wa bango.

Kara karanta wannan

Isra'ila ta kira ruwa, Iran ta kaddamar da sababbin hare hare masu zafi

Iran ta farmaki babban rumbun ajiyar nukiliyar Isra'ila.
Rumbun makamin nukiliyar Isra'ila da ke Dimona, Kudancin saharar Negev. Hoto: THOMAS COEX/AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Sukar makami daga sararin samaniya

Ma'aikacin jinya, Karmel Cohen, ya bayyana cewa wurin da harin ya afka ya rikice sosai kuma an samu barna mai yawa.

Hotunan bidiyo sun nuna wani abu yana faɗowa daga sararin samaniya da matuƙar gudu kafin ya daki birnin, in ji rahoton France 24.

Ko da yake harin ya afka cikin gari, amma halin da rumbun nukiliyar dake kusa da wurin zai shiga, shi ne babban abin fargaba ga duniya.

An gudanar da zanga zanga a Isra'ila

A wani labari, mun ruwaito cewa, an gudanar da wata karamar zanga-zangar ƙin jinin yaƙi a Tel Aviv inda mutane suka yi kira ga Isra'ila ta janye daga harin da ake kai wa Iran.

Wannan na zuwa ne yayin da Iran ta ci gaba da harba makamai masu linzami kan biranen Isra'ila a matsayin martanin kashe manyan kwamandojin yakinta.

Jami'an tsaro a Isra'ila sun tarwatsa masu zanga-zangar saboda dokar ta-ɓaci da kuma fargabar makaman da Iran ke harbawa zai iya fadawa kan su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com