Shugaban Rasha Ya Yi Takaicin Kisan Ali Larijani, Ya Aika Muhimmin Sako ga Jagoran Iran

Shugaban Rasha Ya Yi Takaicin Kisan Ali Larijani, Ya Aika Muhimmin Sako ga Jagoran Iran

  • Kisan da Isra'ila ta yi wa babban jagoran tsaron kasar Musulunci ta Iran, Ali Larijani ya fara jawo hankalin shugabannin kasashen duniya
  • Shugaban Rasha, Vladimir Putin ya nuna alhini tare da aika sakon ta'aziyya ga jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei kan wannan babban rashi
  • Shugaba Putin ya bayyana Larijani a matsayin “abokin kwarai,” na Rasha, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa kawance kasar da Iran

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Moscow, Russia - Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, ya aika da sakon ta’aziyya ga jagoran koli na Iran, Mojtaba Khamenei, bayan kisan babban jami’in tsaro na kasar, Ali Larijani.

Shugaba Putin ya bayyana alhininsa bisa wannan kisa da Isra'ila ta yi, inda ya bayyana marigayi Ali Larijani a matsayin abokin kasar Rasha na kwarai.

Shugaban Rasha, Putin.
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Outin a fadarsa da ke Moscow Hoto: Gavril Grigorov
Source: Getty Images

Shugaban Rasha ya yi bakin cikin kisan Larijani

Kara karanta wannan

Ali Larijani: Jagoran Iran, Mojtaba Khamenei ya dauki zafi, ya tura sako ga Amurka da Isra'ila

Rahoton da tashar Al-Jazeera ta wallafa ranar Laraba, 18 ga watan Maris, 2026, ya nuna cewa Putin ya bayyana bakin cikinsa kan wannan lamari tare da tuna irin alakar da ya taba yi da marigayin.

Tun farko dai a jiya Talata, 17 ga watan Maris, 2026, Isra'ila ta yi ikirarin kashe shugaban Majalisar tsaro na Iran, Ali Larijani, wanda yana daya daga cikin manyan jagorori a Jamhuriyar Musulunci.

Wannan lamari ya girgiza kasar Iran, inda awanni bayan haka gwamnatin Iran ta tabbatar da cewa Larijani ya yi shahada a wasu hare-hare da Isra'ila ta kai.

Yadda Larijani ya hada kan Rasha da Iran

A cikin sakon ta'aziyyar, Shugaba Putin ya bayyana Larijani a matsayin “abokin kwarai,” na Rasha, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa dangantakar hadin gwiwa tsakanin Moscow da Tehran.

Ya kara da cewa tunanin marigayin zai ci gaba da kasancewa a zukatan su saboda gudunmawar da ya bayar wajen karfafa huldar kasashen biyu, cewar rahoton Vanguard.

Tarihin haduwar Putin da Ali Larijani

Rahoton ya kuma nuna cewa shugaban na Rasha ya sha haduwa da Larijani sau da dama a baya, lamarin da ya kara tabbatar da kusancin da ke tsakaninsu a fannin siyasa da tsaro.

Kara karanta wannan

China ta gaza hakuri, ta sake yunkurowa kan yakin Amurka da kasar Musulunci ta Iran

Ana ci gaba da nuna damuwa kan matakin da Isra'ila ke dauka a baya-bayan nan na kashe manyan jagororin kasar Iran da yakin da ke iara tsananta a yankin Gabas ta Tsakiya.

Ali Larijani.
Tsohon shugaban Majalisar tsaron Iran da aka kashe, Ali Larijani Hoto: Anadolu
Source: Twitter

Tun a harin farko, Isra'ila da hadin gwiwar Amurka suka kashe jagorran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei. Yanzu kuma ana ci gaba da kashe manyan kusoshin kar Ta Musulunci.

Putin ya yi magana da shugaban Iran

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban ƙasar Rasha, Vladimir Putin, ya yi wata muhimmiyar tattaunawa ta waya da shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

An tabbatar da cewa Putin ya tattauna da Shugaba Masoud Pezeshkian.kan batun yakin Iran da Isra'ila wanda ya jawo martani daga ko ina a fadin duniya.

Shugaban na Rasha ya kuma bayyana cewa mafita mafi dacewa ita ce warware rikicin ta hanyar siyasa, tattaunawa da diflomasiyya maimakon amfani da karfin soji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262