Iran Ta Sake Jikawa Amurka Aiki, Ta Ruguza Shirin Shugaba Trump ana tsaka da Musayar Wuta

Iran Ta Sake Jikawa Amurka Aiki, Ta Ruguza Shirin Shugaba Trump ana tsaka da Musayar Wuta

  • Da alama tsare-tsaren farko da aka yi na ziyarar da Shugaba Donald Trump zai kai kasar China ya wargaje, har sai an sake sanya wani lokaci
  • Gwamnatin Amurka ta tabbatar da cewa za a samu jinkiri a ziyarar da Shugaba Donald Trump ya shirya kai wa China saboda yakin Iran
  • Mai magana da yawun fadar White House ta ce ba wai soke ganawar Trump da shugaban China, Xi Jinping aka yi ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Amurka - Gwamnatin Amurka ta bayyana cewa akwai yiwuwar a jinkirta taron da aka shirya tsakanin Shugaba Donald Trump da shugaban China, Xi Jinping, sakamakon yaƙin Iran.

Mai magana da yawun fadar shugaban Amurka, White House, Karoline Leavitt ta bayyana cewa babu wani shiri na soke ganawar, amma lokacin gudanar da ita na iya sauyawa.

Kara karanta wannan

'Ba Amurka ba ce,' an gano kasa 1 da take da makullin bude kasuwar mai ta duniya

Trump.
Shigaban kasar Amurka, Donald Trump a fadar White House Hoto: Donald J. Trump
Source: Getty Images

Trump zai jinkirta tafiyarsa zuwa China

Tashar Al-Jazeera ta ruwaito cewa hakan na zuwa ne sakamakon yakin da Amurka ke yi da Jamhuriyar Musulunci ta Iran, wacce ke da kyakkyawar alaka da kasar China.

Leavitt ta ce:

“Mai yiwuwa ne a jinkirta taron, amma ba yana nufin an soke shi gaba daya ba. Matsalar ita ce ta tsara lokaci kawai.”

An shirya gudanar da wannan ganawa tsakanin 31 ga Maris zuwa 2 ga Afrilu, 2026 amma jami’an Amurka sun ce halin da ake ciki na yaƙi na iya sa a sake tsara jadawalin.

Amurka ta fara neman daukin China

Trump ya bayyana cewa Amurka na son China ta taimaka wajen bude mashigar ruwa ta Strait of Hormuz, wadda Iran ta takaita zirga-zirgar jiragen dakon mai a cikinta.

Wannan mashiga na daga cikin muhimman hanyoyin jigilar mai a duniya, domin kusan kashi ɗaya cikin biyar na man fetur na duniya na wucewa ta cikinta.

Kara karanta wannan

Donald Trump ya faɗi lokacin da Iran za ta hau teburin tattaunawa

China na da kusanci da Iran, kuma tana daya daga cikin manyan masu sayen man fetur daga Tehran, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Abin da zai hana Trump tafiya China

Ministan Kudin Amurka, Scott Bessent ya ce wannan jinkirida za a samu ba shi da alaka da wata matsa lamba daga China, sai dai shugaban Amurka na son ci gaba da zama a Washington domin sa ido kan yaƙin Iran.

Ya ce:

"Bai dace ba shugaban ƙasa ya yi tafiya zuwa ƙasashen waje a lokacin yaƙi. Trump na son ci gaba da jagorantar ayyukan yaƙi daga Washington.
Trump da Jinping.
Shugaban Amurka, Donald Trump tare da takwaransa na China, Xi Jinping Hoto: Andrew Caballero Raynolds
Source: Getty Images

Tasirin rufe mashigar Hormuz

Yaƙin da ake yi tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran ya jawo raguwar zirga-zirgar jiragen dakon mai, hare-hare kan wasu jiragen ruwa da barazanar sanya bama-bamai a cikin teku.

Sojojin Amurka sun amince cewa har yanzu ba su iya tabbatar da tsaron mashigar ba gaba ɗaya, lamarin da ya sa Trump ke kira ga sauran ƙasashe su taimaka wajen kare wannan muhimmiyar hanya ta kasuwancin mai.

Trump ya ce Iran na son tattaunawa da Amurka

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Ana cikin gwabza fada, Trump ya fadi bukatar da shugabannin Iran suka nema

A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Donald Trump ya yi ikirarin cew Iran na nuna matuƙar sha’awar fara tattaunawa da Amurka domin kawo karshen yakin da suke yi.

Shugaban kasar ya bayyana cewa duk da Iran na son shiga tattaunawa da Amurka a halin yanzu, amma shi yana ganin har yanzu akwai sauran rina a kaba.

Trump ya kuma sanar da cewa Amurka na tattaunawa da wasu ƙasashe domin ganin an samar da tsarin tsaro a mashigar ruwa ta Hormuz.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262