Gaba da Gabanta: An Samu Kasar da Ta Nuna Trump da Yatsa, An Labtawa Amurka Haraji
- China ta sanar da karin harajin kaso 41% kan kayayyakin Amurka yayin da rikicin cinikayya ya kara tsananta tsakanin kasashen
- Tun da fari, Donald Trump ya kara haraji kan kayan China zuwa 145%, lamarin da China ke kallo a matsayin cin zarafi na tattalin arziki
- Kayayyakin Amurka da sabon harajin zai shafa sun hada da kayan jirage da magunguna yayin da China ta shirya yin karar Trump gaban WTO
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
China - A ranar Juma'a ne kasar China ta sanar da cewa za ta kara haraji kan kayayyakin da ake shigowa da su daga Amurka daga kashi 84% zuwa 125%.
Wannan na zuwa ne yayin da rikicin cinikayya ke kara kamari tsakanin manyan kasashen tattalin arziki na duniya guda biyu.

Asali: Twitter
Rigima tsakanin Amurka da China ta jefa kasuwanni cikin rudani tare da haifar da fargabar durkushewar tattalin arzikin duniya, inji rahoton AP News.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alaka tsakanin China da Amurka ta kara kamari
Yayin da shugaban Amurka Donald Trump ya dakatar da harajin shigo da kaya daga wasu kasashe a wannan makon, ya kara wa China haraji zuwa kashi 145%.
China ta soki matakin Trump da cewa "cin zarafin tattalin arziki" ne, inda ta yi alkawarin mayar da martani ta hanyar kara haraji kan kayan Amurka, da zai fara aiki daga ranar Asabar.
A cikin wata sanarwa, mai magana da yawun ma’aikatar kudi ta China ya bayyana cewa karin harajin da Amurka ke yawan yi zai zama abin dariya a tarihin tattalin arzikin duniya.
Sai dai ya kara da cewa, “idan Amurka ta dage wajen ci gaba da tauye muradun China, to China za ta dauki mataki mai karfin gaske, har sai ta tabbatar da gaskiya.”
Ma’aikatar kasuwancin China ta ce za ta shigar da kara a hukumance gaban hukumar kasuwanci ta duniya (WTO) kan harajin da Amurka ta kakabawa kayayyakinta.
China ta kara haraji kan wasu kayan Amurka
Sababbin matakan harajin Trump sun haifar da tashin hankali a kasuwannin hannayen jari da na bashi, inda wasu ke fargabar hakan na iya jefa Amurka cikin durkushewar tattalin arziki.
Kodayake an samu dan sassauci lokacin da Trump ya dakatar da wasu haraji ga wasu kasashe, amma ana ci gaba da damu kan tabarbarewar alakar kasuwanci tsakanin Amurka da China.
Time Magazine ta rahoto shugabar WTO, Ngozi Okonjo-Iweala, ta ce rikicin cinikayya tsakanin Amurka da China “na iya janyo mummunan tasiri ga ci gaban tattalin arzikin duniya.”
Sabbin harajin na China za su shafi kayayyaki irin su wake, jiragen sama da sassan su, da magunguna, wadanda ke cikin manyan kayayyakin da China ke shigowa da su daga Amurka.
Yadda sabon harajin China zai shafi Amurka

Asali: Getty Images
A makon da ya gabata, Beijing ta dakatar da shigo da dawa, kaji da sauransu daga wasu kamfanonin Amurka, tare da kara takunkumi kan fitar da albarkatun kasa masu matukar muhimmanci ga fasahohi daban-daban.
Daga bangaren Amurka kuma, manyan kayayyakin da take shigo da su daga China sun hada da na’urorin lantarki kamar kwamfutoci da wayoyin salula, injinan masana’antu da kayan wasanni, wanda hakan zai iya haifar da karin farashi ga ‘yan kasuwa da mutane, duba da yadda harajin ya kai 145%.
A ranar Laraba ne Trump ya sanar da cewa za a kakabawa China haraji na 125%, amma bai hada da karin haraji na 20% ga sinadarin fentanyl da China ke hadawa ba.
Nigeria ta hana kayan Amurka shigowa kasar
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin Amurka ta soki matakin Najeriya na haramta shigo da kayayyaki 25, tana mai cewa hakan yana tauye ribar ‘yan kasuwarta.
Wannan martanin ya biyo bayan karin haraji da Donald Trump ya sanya makon da ya gabata, inda Najeriya ta fuskanci karin haraji na kashi 14.
Ofishin harkokin kasuwancin Amurka (USTR) ya bayyana cewa dokar da Najeriya ta kafa na hana wasu kaya shigowa na haifar da tsaiko a cinikayya da rage kudaden shiga.
Asali: Legit.ng