Jerin Sunayen Manyan Masu Kudin Duniya 10 Yayin da Elon Musk Ya Rasa Matsayinsa

Jerin Sunayen Manyan Masu Kudin Duniya 10 Yayin da Elon Musk Ya Rasa Matsayinsa

  • Attajirin biloniya Elon Musk ya sake rasa babban matsayinsa a jerin masu kudin duniya a shekarar 2024
  • Yanzu Bernard Arnault ne ke zaune a matysayin mai kudin duniya da ke raye, inda ake lissafin dukiyarsa ta kai dala biliyan 223.3, ya kere Elon Musk
  • Musk, wanda shine mai kudin duniya a baya, ya koma matsayin na biyu, sai Jeff Bezos da Mark Zuckerberg

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Dukiyar masu kudin duniya zuwa ranar Laraba, 21 ga watan Fabrairun 2024, ta kai sama da dala tiriliyan 1.52.

Wannan ta yi kasa da dala biliyan 9.5 idan aka hada lissafin dukiya ta dala tiriliyan 1.53 da manyan masu kudin duniya 10 suka fara da ita a Janairun 2024.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta gaji, ta shirya binciken bashin N23tr da Emefiele ya ba gwamnatin Buhari

Masu kudin duniya
Jerin Sunayen Manyan Masu Kudin Duniya 10 Yayin da Elon Musk Ya Rasa Matsayinsa Hoto: Thierry Monasse
Asali: Getty Images

Jerin attajirai ya sauya

A bisa bayanan da mujallar Forbes ta fitar, biloniyan Faransa Bernard Arnault ya zama mai kudin duniya, da darajar dukiyar da ta kai dala biliyan 223.3 zuwa ranar Laraba, 21 ga watan Fabrairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan ya fara shekarar a matsayin na biyu da dukiyar da ta kai dala biliyan 203.3, arzikin Arnault ya karu da dala biliyan 20.1.

Elon Musk, shugaban kamfanin Tesla da SpaceX kuma shugaban dandalin X (wanda aka fi sani da Twitter a baya), ya sauka zuwa matsayin na biyu da dukiyar da ta kai dala biliyan 205.5 zuwa ranar 21 ga watan Fabrairun 2024.

Wannan na nuna ragowa sosai daga dala biliyan 250.4 na arzikin da yake da shi a ranar 1 ga watan Janairun 2024, wanda ke nuna ragin dala biliyan 44 zuwa yanzu a 2023.

Kara karanta wannan

Yajin aikin direbobin tanka: Matashi ya koka yayin da ya siya fetur kan N1,000 lita a jihar PDP

Jerin masu kudin duniya a zuwa Laraba, 21 ga watan Fabrairu

  1. Bernard Arnault da zuri'arsa - Dala biliyan 223.3
  2. Elon Musk - Dala biliyan 205.5
  3. Jeff Bezos - Dala biliyan 188.4
  4. Mark Zuckerberg - Dala biliyan 166.1
  5. Larry Ellison - Dala biliyan 136.1
  6. Warren Buffett - Dala biliyan 133.9
  7. Bill Gates - Dala biliyan 123.8
  8. Steve Ballmer - Dala biliyan 120.3
  9. Larry Page - Dala biliyan 118.3
  10. Mukesh Ambani - Dala biliyan 113.9

Kamfanonin Najeriya 3 sun tafka asara

A wani labari na daban, mun ji cewa wasu kamfanoni guda uku karkashin rukunin 'kamfanonin da ke sarrafa kayan da aka fi amfani da su (FMCG) sun tafka asarar sama da naira biliyan 140.

Kamfanonin da suka hada da kamfanin abinci na BUA, Flourmills da Cadbury Plc sun yi asarar ne sakamakon karyewar darajar Naira a shekarar da ta gabata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel