Kungiyar Hamas Ta Falasdinu Ta Kai Hari Kan Isra'ila

Kungiyar Hamas Ta Falasdinu Ta Kai Hari Kan Isra'ila

  • Ƙungiyar Hamas mai rajin kare Falasɗinawa ta ƙaddamar da hare-hare a kan Isra'ila da sanyin safiyar ranar Asabar
  • Hare-haren na ƙungiyar Hamas su ne mafi muni tun bayan yaƙin kwanaki 11 da aka gwabza tsakaninsu da Isra'ila a shekarar 2011
  • Rundunar sojin Isra'ila ta tabbayar da aukuwar harin amma ba ta faɗi adadin mutanen da suka mutu ba

Isra'ila - Ƙungiyar Hamas da ke rajin kare Falasɗinawa ta ƙaddamar da hare-hare a kan Isra'ila.

Harin wanda ta yi wa laƙabi da suna "Operation Al-Aqsa Flood", shi ne mafi muni tun bayan yaƙin kwanaki 11 da Isra'ila da Hamas suka yi a shekarar 2021, cewar rahoton CBS News

Kungiyar Hamas ta kai Hari a Isra'ila
Kungiyar Hamas ta kaddamar da hare-hare a Isra'ila Hoto: AFP
Asali: Twitter

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta ƙaddamar da atisayen "Operation Iron Swords" kan ƙungiyar Hamas a zirin Gaza.

Harin wanda aka kai da sanyin safiyar ranar Asabar, 7 ga watan Oktoba, ya auku ne a lokacin Simchat Torah, wani hutu da ya faɗo a ƙarshen bikin Yahudawa na mako guda da ake kira Sukkot.

Kara karanta wannan

Dubu Ta Cika: An Kama Babban Malami da Wani Mutumi Kan Muhimmin Abu 1 a Birnin Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An harba rokoki har zuwa arewacin Tel Aviv. Hamas ta kuma aike da mayaƙa zuwa Kudancin Isra'ila, rahoton Times of Israel ya tabbatar.

Kafofin yada labaran Isra'ila sun ce wasu masu ɗauke da bindigu sun buɗe wuta kan masu wucewa a garin Sderot, kuma hotunan da ke yawo a shafukan sada zumunta sun nuna yadda ake gwabza faɗa a titunan birnin da kuma wasu masu ɗauke da bindigu da ke cikin motocin jeeps suna yawo a cikin karkara.

Muna cikin yaƙi, sojojin Isra'ila

Sojojin Isra'ila sun ce suna yaƙar mayaƙan Hamas a Gaza da suka shiga Isra'ila ta ƙasa da ruwa da kuma ta sama ta hanyar amfani da jiragen sama a ranar Asabar, bayan da aka harba makamin roka kan Isra'ila daga yankin Falasdinu.

Kakakin rundunar sojin Isra'ila Richard Hecht ya shaidawa manema labarai cewa:

Kara karanta wannan

'Dan Majalisar Tarayya Ya Kai Koken 'Yan Arewa, Ya Faɗi Hanyar Kawo Karshen Matsalar Tsaro

"Shiryayyen harin an kai shi ne ta ƙasa da sama da ruwa. A yanzu haka muna ƴaƙi. Muna fafatawa a wasu wurare da ke kusa da zirin Gaza… a yanzu sojojinmu suna fada ta ƙasa a Isra’ila"

Hecht ya tabbatar da cewa an samu asarar rayuka, amma ba zai bayar da cikakken bayani ba, ko magana akan rahotannin da ke cewa mayaƙan Hamas sun cafke Isra'ilawa da dama.

Sojoji Sun Yi Yunkurin Juyin Mulki

A wani labarin kuma, sojoji sun yi yunkurin kifar da gwamnatin sojoji ta ƙasar Burkina Faso, a ranar Laraba, 27 ga watan Satumba.

Sai dai, sojojin ƙasar sun samu nasarar daƙile ynuƙurin juyin mulkin tare da cafke waɗanda ake zargi da kitsa shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel