Bayan Shekaru Fiye Da 30 Yana Jogorantar Sallah, Shuraim Ya Yi Bankwana Da Limanci A Masallacin Makkah

Bayan Shekaru Fiye Da 30 Yana Jogorantar Sallah, Shuraim Ya Yi Bankwana Da Limanci A Masallacin Makkah

  • Daya cikin limaman dindindin na masallacin Harami da ke Makka, Sheikh Saud Ash Shuraim ya yi bankwana da limanci
  • Hakan ta tabbata ne biyo bayan fitar da sunayen limaman da za su jagoranci sallar Tarawi na azumin bana kuma babu sunansa
  • A yan kwanakin baya, Sheikh Shuraim ya nemi a bashi uzurin yin murabus din da aka ce ya nema don kashin kansa

Saudiyya - Yanzu babu sauran shakku kan cewa Sheikh Saud Ash Shuraim ya dena limanci a mallacin Ka'abbah da ke kasar mai tsarki ta Saudiyya, rahoton BBC Hausa.

An tabbatar da hakan ne yayin da hukumar da ke kula da masallatai mafiya tsarki biyu na duniya wato masallacin Makkah da Madina ta saki jerin sunayen limaman da za su jagoranci sallar Tarawi, amma sunasa ba ya ciki.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Farashin danyen mai ya fadi a kasuwar duniya, zai shafi Najeriya

Shuraim
Sheikh Saud Ash Shuraim Ya Dena Limanci A Masallacin Makkah. Hoto: Haramain Sharifain
Asali: Facebook

A baya, tun dai a watan Janairu rahotanni sun fito da ke cewa limami guda daya cikin shahararrun limaman manyan masallatan biyu zai ajiye aiki.

Sai dai a watan Fabrairun 2023 ne bayanai suka fito fili cewa Sheikh Saud Ash Shuraim ne limamin da zai ajiye aiki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Fitaccen limamin ya yi kimamin shekaru 32 yana jagorantar sallah a Saudiyya.

A ranar 12 ga watan Rabi Al Awal na 1443 wato Litinin 18 ga watan Oktoban shekarar 2021 ne Shuraim ya ja sallarsa ta karshe a masallacin Ka'abah.

Abin da yasa Shuraim ya yi murabus

A hukumance ba a sanar da dalilin da yasa babban limamin ya ajiye aiki ba duk da cewa yana da sauran karfinsa, sai dai wasu kafofi sun rahoto cewa shi da kansa ne ya bukaci zai dena limancin.

Kara karanta wannan

NDLEA Ta Aika Muhimmin Sako Ga Masu Neman Aikin da Hukumar Za Ta Dauka

Takaitaccen tarihin Shuraim

Bayanai sun nuna cewa an haifi Sheikh Sa’ud Ibn Ibrahim Ibn Muhammad Al-Shuraim a ranar 19 ga watan Janairun 1964 a Riyadh, Saudiyya.

Ya yi karatun firamare a Areen Elementary School ya kuma yi sakandare a Modern School for Secondary Education.

Daga bisani ya cigaba da karatun sakandare a Al-Yarmouk North High School, ya kammala a 1983.

Ta tafi jami'ar Imam Muhammad Bin Saud, ya yi digiri a 1988.

Bai tsaya nan ba, ya cigaba da zurfafa karatu har sai da ya samu digirin digirgir.

An Bude Birnin At-Turaif A Saudiyya

A wani rahoton, kun samu rahoto cewa a ranar 4 ga watan Disamban 2022, Saudiyya ta sanar da bude tsohon birni mai tarihi na At-Turaif.

Kamar yadda BBC Hausa ta rahoto, za a bude birnin ne domin mutane masu zuwa yawon bude ido wadanda ke sha'awan tarihin kasar.

Kara karanta wannan

Farashin Man Fetur Zai Lula, Gwamnatin Tarayya Tana Shirin Barin Tinubu da Jan Aiki

Asali: Legit.ng

Online view pixel