UNGA77: Shugaba Buhari Yayi Bankwana da Shugabannin Kasashen Duniya

UNGA77: Shugaba Buhari Yayi Bankwana da Shugabannin Kasashen Duniya

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi bankwana da shugabannin kasashen duniya a taron majalisar dinkin duniya karo na 77
  • Yace a taron majalisar karo na 78, wata sabuwar fuska zasu gani matsayin shugaban kasar Najeriya saboda zaben da za a yi
  • Shugaban kasan yace abinda yake da tabbacin mulkinsa zai bari shi ne zaban gaskiya da adalci a Najeriya

A ranar Larabar da ta gabata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shaidawa shugabannin duniya cewa gwamnatinsa ta kuduri aniyar samar da tsarin zabe na gaskiya da adalci wanda zai kawo sabon shugaban kasa a shekara mai zuwa.

Ya kara tabbatar da cewa sabuwar fuska ce za ta wakilci Najeriya a taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78 a shekarar 2023 mai zuwa.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: An cimma matsaya tsakanin ASUU da majalisa, za a kai batu gaban Buhari kafin a koma makaranta

Muhammadu Buhari
UNGA77: Shugaba Buhari Yayi Bankwana da Shugabannin Kasashen Duniya. Hoto daga Punchng.com
Asali: UGC

Buhari ya yi wadannan kalaman ne a jawabinsa na karshe a matsayin shugaban kasa a taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 77 da aka gudanar a birnin New York na kasar Amurka, Jaridar Punch ta rahoto.

"Daya daga cikin abubuwan da zan gadar shi ne zabe na gaskiya da adalci a 2023. Kuma za ku ga sabuwar fuska a nan tana magana a matsayin Najeriya a UNGA ta 78."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

- Buhari yace.

Ya kara da yin kira da a sassauta nauyin basussuka ga kasashe masu karamin karfi da kuma soke basussuka kai tsaye ga jihohin da ba su iya biyan basussukan, irin kiran da ya yi a bara a taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 76.

Buhari ya kara da gode wa shugabannin kasashen duniya da suka ba Najeriya hadin kai a kokarin tunkarar kalubale daban-daban tare da bayyana kokarin gwamnatinsa na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin yammacin Afirka.

Kara karanta wannan

Inyamuri ba zai gaji Buhari ba, gwamnan yankin Kudu ya bayyana dalilai

Buhari Ya Nada Kwarrren Dan Jarida Matsayin Sabon Shugaban NTA Na Kasa

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya nada Mr Salihu Dembos a matsayin direkta-janar/babban shugaba na Gida Talabijin Na Najeriya, NTA.

Ministan Sadarwa da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba a Abuja, The Punch ta rahoto.

Ya ce nadin da aka masa na tsawon shekaru uku ne a karon farko.

Asali: Legit.ng

Online view pixel