Bidiyon Babur Mai Tashi Sama na Farko da aka Kera a Duniya, Za a Siyar da shi Sama da N300m

Bidiyon Babur Mai Tashi Sama na Farko da aka Kera a Duniya, Za a Siyar da shi Sama da N300m

  • Babur din farko a duniya mai tashi sama mai suna XTURISMO, wanda ake ta siyarwa a kasar Japan, ya bayyana a Amurka a karon farko
  • Yayin gwada shi, Thad Szott ya tabbatar da cewa akwai natsuwa yayin da mutum ke tashi sama a babur din da za a siyar kan $777,000 (N338,383,500.00)
  • Mutane da yawa sun yi martani kan bidiyon inda suka bayyana cewa nesa ta zo kusa, yayin da wasu suka ce yayi kama da wani mashin a fim din Star Wars

Reuters ta rahoto cewa, XTURISMO shi ne babur na farko a duniya mai tashi sama yayin da aka gwada aikinsa a Amurka.

Kamar yadda rahoto daga kafar yada labaran ta bayyana, babur din zai iya lulawa sararin samaniya ya kwashe mintuna 40 yayin da yake zura gudu a kan mita 62 duk sa'a daya.

Kara karanta wannan

Ka latsa ni: Kyakkyawar budurwa ta tari wani dan Najeriya, ta nemi su fara soyayya

Babur mai tashi sama
Bidiyon Babur Mai Tashi Sama na Farko da aka Kera a Duniya, Za a Siyar da shi Sama da N300m. Hoto daga @reuters
Asali: Twitter

Tuni ake amfani da babur mai tashi sama a Japan

Duk da na fara siyar da shi a kasar Japan, za a saki karaminsa a Amurka nan da shekarar 2023 kuma ana kiyasin kudinsa zai kama $777,000 (N338,383,500.00).

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Thad Szott, mutumin da ya gwada tashi da babur din sama yace akwai natsuwa a lamarin kuma babur din baya girgiza yayin da ake sararin samaniya. Wani kamfanin kasar Japan mai suna AERWINS ne ya kera babur din.

Ga bidiyonsa:

Jama'a sun yi martani

Legit.ng ta tattaro muku wasu daga cikin martanin jama'a

@escayola yace:

"Nesa ta zo kusa, na dade ina jiran wannan lokacin duk tsawon rayuwata.

@cpk_kc yace:

"Idan wannan nau'in babur ne, toh babu shakka dokin babur ne mai jini."

@Investacus ya tambaya:

"Toh yaushe zamu iya samun Star Wars speedsters?"

Kara karanta wannan

‘Yan Kasuwa Na Lissafin Sayen Mai a N148, Tinubu Ya Dage a Cire Tallafin Fetur

@jedicathy tace:

"Yanzu ina su jedi"

@TeamTapey yace:

"Wannan ne zai zama babur dina na gaba."

Cikin Sa'o'i 8 Kacal, Dangote ya Tafka Asarar N9.42b, Arzikinsa Ya Koma Kamar na 2021

A wani labari na daban, hamshakin mai arzikin Afrika, Alhaji Aliko Dangote ya tafka asara inda dukiyarsa tayi kasa wanda bata taba yi ba a cikin watanni 12, kuma a halin yanzu dukiyarsa $18.8 biliyan ce cif.

Wannan ya faru ne bayan da $22.0 miliyan na dukiyarsa suka lalace a cikin kasuwanci cikin sa'o'i takwas kacal a ranar Laraba, 14 ga watan Satumban 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel