'Yan Sanda Sun Kama Wani Kwararren Likita Dake Kashe Majinyata Don Sace Motocinsu

'Yan Sanda Sun Kama Wani Kwararren Likita Dake Kashe Majinyata Don Sace Motocinsu

  • Jami'an hukumar yan sanda reshen jihar Edo sun kama wani kwararren Likita dake kashe Direbobi don ya sace Motocinsu
  • Kakakin hukumar yan sanda, SP Nwabuzor, yace Likitan mai suna, Abbas Adeyemi, ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi
  • Tuni dai aka gurfanar da wanda ake zargin a gaban Kotun domin ɗaukar mataki, a cewar hukumar yan sanda

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Edo - Rundunar 'yan sanda a jihar Edo tace dakarunta sun kama wani kwararren likiri wanda ya kware wajen sace Motocin Taxi bayan yi wa Direbobin Allurar da zata zama ajalinsu.

Premium Times tace Likitan mai suna, Abbas Adeyemi, ɗan shekara 36, yana aiki ne a babban Asibitin Kaiama da ke jihar Kwara, arewa ta tsakiya a Najeriya.

Likitan ya amsa laufin cewa yana yin awon gaba da mutocin mutanen bayan ya sanƙama musu Allura, a cewar hukumar 'yan sanda.

Kara karanta wannan

‘Yan Sanda Sun Cafke Likita Mai Yin Allurar Mutuwa, Ya Sace Motocin Marasa Lafiya

Dakarun yan sandan Najeriya.
'Yan Sanda Sun Kama Wani Kwararren Likita Dake Kashe Majinyata Don Sace Motocinsu Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Mai magana da yawun hukumar yan sandan Edo, Chidi Nwabuzor, ya bayyana cewa Likita Adeyemi, mahaifin yara biyu, ya fito ne daga Offa, jihar Kwara.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda Likitan ke gudanar da kazamar sana'arsa

SP Nwabuzor, yace wanda ake zargin ya amsa cewa shi ne ya yi ajalin wani direban Taxi, Emmanuel Yobo, a jahar Edo. Likitan ya kashe Yobo, dan shekara 39 ranar 3 ga watan Satumba, bayan ɗirka masa Allurai.

A haɗuwar Likitan da Yobo na farko, ya nemi Direban ya taimaka masa wajen sayar da wata Mota da ya zo da ita jihar yayin da a haɗuwa ta biyuya kashe shi.

A jawabin kakakin yan sandan yace:

"Ranar 3 ga watan Satumba (karo na biyu da suka haɗu) ya nemi Direban ya zagaya da shi buɗe ido a birnin Benin, inda ya ɗirka masa Allurai a jikinsa, suka masa illa har rai ya yi halinsa."

Kara karanta wannan

Soyayyar Zamani: Masoya Sun Sayar Da Jaririn Da Suka Haifa Kafin Fatiha Kan N500,000

A cewar 'yan sanda, wanda ake zargin ya watsar da gawar Mamacin a gefen titin Benin-Ondo, kana ya yi awon gaba da motarsa, Toyota Camry.

Kakakin yan sanda yace bincike da sashin yaƙi da garkuwa da aikata manyan laifuka na hedkwatar yan sanda dake Benin ya gudanar, ya taimaka har aka cafke Likitan kuma aka kwato motar a Osogbo, jihar Osun.

"Da aka tsananta bincike yan sanda sun gayyaci wanda ya sayi Motar kuma ya yi bayanin yadda Likita ya zo da Motar daga jihar Kwara, a cewarsa sayenta ya yi."

Kakakin yan sanda ya ƙara da cewa wanda ake zargin ya amsa laifin kashe wani Diereban Taxi ɗin na daban. Tuni aka gufanar da shi a gaban Kotu.

A wani labarin kuma Gaskiya Ta Fito Kan Ƙishin-Ƙishin Ɗin Tukur Mamu Ya Fallasa Masu Ɗaukar Nauyin 'Yan Ta'adda a Arewa

Mun gudanar da binciken gano gaskiya kan wani rubutu da ake yaɗawa a Facebook da wasu kafafen sada zumunta kan Tukur Mamu.

Kara karanta wannan

Dan Sarki A Najeriya Ya Gayyaci 'Ƴan Kungiyar Asiri' Su Kashe Mahaifinsa Saboda Wata Sabani

Rubutun dai ya yi ikirarin cewa mai shiga tsakanin yan ta'adda da FG don sako Fasinjojin jirgin Kaduna ya fallasa sunayen masu ɗaukar nauyin ta'addanci a arewacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel