Da Duminsa: Fadar Buckingham Ta Sanar da Ranar Birne Sarauniya Elizabeth II
- Fadar Buckingham ta bayyana ranar Litinin 19 ga watan Satumba matsayin ranar da za a birne sarauniya Elizabeth II
- Kamar yadda aka bayyana, za a ajiye akwatin gawarta a dakin taro na Westminster tun ranar Laraba domin jama'a sun yi ganawar karshe da ita
- Daga nan za a fara bikin birneta wurin karfe 11 na safe a Landan inda daya daga cikin manyan limaman addinin Kiristanci zai jagoranta
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Fadar Buckingham ta sanar da cewa za a birne sarauniya Elizabeth II a ranar 19 ga watan Satumban 2022.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa, sarauniya Elizabeth II ta mutu a ranar Alhamis da ta gabata yayin da take da shekaru 96 a duniya.
Manyan mutane a fadin duniya sun cigaba da mika sakonnin ta'aziyyarsu na mutuwar marigaiyar da ta dade a karagar mulkin Birtaniya.

Kara karanta wannan
A Sauya Sunan Aso Rock Ko Sauran Yankunan Arewa Zuwa Sunan Sarauniya Elizabeth, Ohanaeze Ga FG

Asali: UGC
A daya bangaren, Sarki Charles na III ya tabbata sabon Sarkin Ingila a hukumance a ranar Asabar da ta gabata.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kamar yadda fadar Buckingham ta bayyana, za a yi jana'izar Sarauniya Elizabeth II a birnin Landan wurin karfe 11 na safe, 19 ga watan Satumba.
Za a ajiye akwatin gawar marigayiyar sarauniyar a Westminster Hall tun daga ranar Laraba inda za a bai wa jama'a damar ganawa da ita a karon karshe.
Ana tsammanin ko dai Dean na Westminster ko Archbishop na Canterbury, babban bishop na cocin Ingila ne zai jagoranci jana'izarta.
Kyawawan Hotunan Lokuta da Rayuwar Marigayiyar Sarauniya Elizabeth II
A wani labari na daban, Ingila ta fada makoki a ranar Alhamis, 8 ga watan Satumban 2022 bayan labarin mutuwar sarauniya Elizabeth Alexandra Mary wacce ta kasance sarauniyar da ta fi kowanne sarki dadewa a kujerar sarautar Birtaniya.
Mahaifiya kuma kakar an haifeta a ranar 21 ga watan Afirilin 1926 a titin Bruton dake Landan, UK ga tsohon Duke din York, Yarima Albert da matarsa Elizabeth Bowes-Lyon.
Kamar yadda takardar da fadar Buckingham ta fitar ta bayyana,sarauniyar ta tabbata basarakiyar da tafi dadewa a kujerar tun a 2015 yayin da ta wuce shekarun da Sarauniya Victoria tayi a kujerar.
Sarauniya Elizabeth ta rasu ta bar 'ya'yanta da suka hada da Yariman Wales, Yarima Charles, Duke din York, Yarima Andrew da Gimbiya Anne, Sai Yarima Andrew wanda shi ne Earl din Wessex tare da jikoki da suka hada da Yarima William da Yarima Harry sai tattaba kunne masu yawa.
Asali: Legit.ng