Kyawawan Hotunan Lokuta da Rayuwar Marigayiyar Sarauniya Elizabeth II

Kyawawan Hotunan Lokuta da Rayuwar Marigayiyar Sarauniya Elizabeth II

Ingila ta fada makoki a ranar Alhamis, 8 ga watan Satumban 2022 bayan labarin mutuwar sarauniya Elizabeth Alexandra Mary wacce ta kasance sarauniyar da ta fi kowanne sarki dadewa a kujerar sarautar Birtaniya.

Mahaifiya kuma kakar an haifeta a ranar 21 ga watan Afirilin 1926 a titin Bruton dake Landan, UK ga tsohon Duke din York, Yarima Albert da matarsa Elizabeth Bowes-Lyon.

Kamar yadda takardar da fadar Buckingham ta fitar ta bayyana,sarauniyar ta tabbata basarakiyar da tafi dadewa a kujerar tun a 2015 yayin da ta wuce shekarun da Sarauniya Victoria tayi a kujerar.

Elizabeth II
Kyawawan Hotunan Lokuta da Rayuwar Marigayiyar Sarauniya Elizabeth II. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Sarauniya Elizabeth ta rasu ta bar 'ya'yanta da suka hada da Yariman Wales, Yarima Charles, Duke din York, Yarima Andrew da Gimbiya Anne, Sai Yarima Andrew wanda shi ne Earl din Wessex tare da jikoki da suka hada da Yarima William da Yarima Harry sai tattaba kunne masu yawa.

Kara karanta wannan

Tarihin Sarki Charles III, Wanda Ya yi Shekaru 70 Yana Jiran Gadon Sarauta

Ta gaji karagar mulkin daga Edward VII ta bangaren mahaifinta a ranar 11 ga watan Disamban 1936. Mahaifinta ya zama Sarki George na VI inda ta kasance gimbiya mai jiran gado.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Aurenta

Ta Auri Laftanal Philip a ranar 20 ga watan Nuwamban 1947 wanda a ranar aurensu aka bashi sarauta uku ta Duke na Edinburgh, Earl na Merioneth da Baron Greenwich.

Wannan ya faru ne bayan ya ajiye sarautarsa ta Girka tare da zama 'dan kasar Birtaniya, Punch ta rahoto.

Ma'auratan sun hadu a 1939 yayin da 'ya'yan sarautar suka ziyarci kwalejin Dartmouth ta sojin ruwa kuma sun haifa Yarima Cahrles a ranar 14 ga watan Nuwamban 1948.

Yarima Philip ya mutu ya bar Sarauniya Elizabeth II a ranar 9 ga watan Afirilun 2021 bayan kwashe shekaru 73 da suka yi suna zaman aure.

Kara karanta wannan

Taikaitattun bayanai masu kayatarwa da ya kamata ku sani game da sarauniyar Ingila Elizabeth

Elizabeth II
Kyawawan Hotunan Lokuta da Rayuwar Marigayiyar Sarauniya Elizabeth II. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Gogewarta a harkokin sarauta

Kafin hawanta karagar mulki, Elizabeth ta wakilci mahaifinta a taruka daban-daban lokacin da lafiya tayi masa karanci.

A wannan lokacin, an bata mukamin kanal amma na girmamawa a cikin dakarun gidan sarautar. Ta zama laftanal ta biyu a bangaren mata na sojojin Birtaniya.

Rasuwar mahaifinta

Tare da rakiyar mijinta, ta yi rangadi zuwa Austarlia da New Zealand a 1952 kuma a yayin da take kan hanyarta ta zuwa Kenya ne ta samu labarin mutuwar mahaifinta wanda ya faru a ranar 6 ga Fabrairun 1952.

Kansar huhu ta yi ajalinsa yana da shekaru 56 yayin da Elizabeth ta zama sarauniya kuma aka yi nadinta a ranar 2 ga watan Yunin 1952 a Westminster Abbey a taron da sama da mutum miliyan 20 suka kalla a duniya.

Elizabeth II
Kyawawan Hotunan Lokuta da Rayuwar Marigayiyar Sarauniya Elizabeth II. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Kalubalen da ta fuskanta a rayuwa

Gidan sarautar karkashin Sarauniya Elizabeth bai tafi kalau babu wasu cece-kuce ba. a 1968, Sarauniya Elizabeth 11 ta bada dama an nadi bidiyon rayuwarta na tsawon wata biyu inda aka fitar da shi wanda sama da mutum miliyan 30 suka kalla.

Kara karanta wannan

Labari mara dadi: Allah ya yiwa Sarauniyar Ingila rasuwa bayan gajeriyar rashin lafiya

Wannan ne ya bude sirrin gidan sarautar inda aka gane cewa rayuwa suke yi kamar kowa.

Manyan damuwar da suka sameta

A 1992, basarakiyar ta shiga damuwa bayan mace-macen aure sun fada gidan sarautar inda auren 'ya'yan uku ya mutu.

Yarima Charles ya rabu da matarsa Gimbiyar Wales Diana, Yarima Andre ya rabu da matarsa Sarah Duchess din York, Anne ta saki mijinta Mark Philips.

Gidan sarautar ya sake fadawa cikin tashin hankali bayan Diana ta rasu a ranar 31 ga watan Augustan 1997 a hatsarin mota a Paris.

A cikin kwanakin nan ne jikan sarauniyar, Yarima Harry da matarsa suka bar fadar da gidan sarautar inda suka koma Amurka.

Makokinta da birneta

Za a kwashe kwanaki ana makoki inda za a birneta bayan kwanaki 10 da mmutuwarta. Za a birne basarakiyar a St.George's Chapel dake Windsor Castle inda aka birne mahaifinta Sarki George VII,'yar uwarta Gimbiya Margaret da mijinta Yarima Philip.

Kara karanta wannan

Da Dumi-dumi: Sarauniyar Ingila Na Gab Da Shekawa Barzahu, Likitoci Sun Fadi Mafita

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel