Sarki Charles Ya Bayyana Irin Mulkin da Zai Yi Wa Jama'arsa

Sarki Charles Ya Bayyana Irin Mulkin da Zai Yi Wa Jama'arsa

  • Sarki Charles III, sabon basaraken da ya gaje marigayiyar mahaifiyarsa, Elizabeth II ya yi jawabin farko bayan zamansa sarki
  • Ya bayyana cewa, a karkashin mulkinsa zai tabbatar ya mulki na kasa da shi da biyayya, mutuntawa da kauna
  • Basaraken ya sanar da cewa babu shakka zai kiyaye kundin tsarin mulkin masarautar da dukkan zuciyarsa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Sarki Charles III, sabon sarkin Birtaniya, ya sha awalshin bautawa jama'arsa da kasashen dake karkashin mulkinsa da biyayya, mutuntawa da kauna har karshen mulkinsa.

Yarima Charles ya bayyana hakan a jawabin da yayi kuma aka nada a Blue Drawing Room dake fadar Buckingham a ranar Juma'a.

Yarima Charles
Sarki Charles Ya Bayyana Irin Mulkin da Zai Yi Wa Jama'arsa. Hoto daga Reuters
Asali: Getty Images

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa, Yace zai tabbatar da dukkan dokokin kundin tsarin mulki na kasar da zuciya daya.

"Kamar yadda sarauniya ta da dukkan iyawarta, ni ma na sha alwashin a tsawon lokacin da Ubangiji ya bani, zan tabbatar da ne rike tsarin kundin tsarin mulkin kasarmu da zuciya daya.

Kara karanta wannan

Kayan duniya: Wasu kadarori masu ban al'ajabi da sarauniya Ingila ta mutu ya bar wa magajinta

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Kuma duk inda zaka rayi a Ingila, ko a karkashin mulkina da iyakokina na duniya, kuma ko me ya kasance tushenka ko addininka, zan dage wurin bauta maka da biyayya, mutuntawa da kauna kamar yafdda na saba har tsawon rayuwata."

- Sarki Charles III ya tabbatar.

Kyawawan Hotunan Lokuta da Rayuwar Marigayiyar Sarauniya Elizabeth II

A wani labari na daban, Ingila ta fada makoki a ranar Alhamis, 8 ga watan Satumban 2022 bayan labarin mutuwar sarauniya Elizabeth Alexandra Mary wacce ta kasance sarauniyar da ta fi kowanne sarki dadewa a kujerar sarautar Birtaniya.

Mahaifiya kuma kakar an haifeta a ranar 21 ga watan Afirilin 1926 a titin Bruton dake Landan, UK ga tsohon Duke din York, Yarima Albert da matarsa Elizabeth Bowes-Lyon.

Kamar yadda takardar da fadar Buckingham ta fitar ta bayyana,sarauniyar ta tabbata basarakiyar da tafi dadewa a kujerar tun a 2015 yayin da ta wuce shekarun da Sarauniya Victoria tayi a kujerar.

Kara karanta wannan

Shugaban wata kasa mai karfin iko ya ce ba zai halarci bikin bison sarauniyar Ingila ba

Sarauniya Elizabeth ta rasu ta bar 'ya'yanta da suka hada da Yariman Wales, Yarima Charles, Duke din York, Yarima Andrew da Gimbiya Anne, Sai Yarima Andrew wanda shi ne Earl din Wessex tare da jikoki da suka hada da Yarima William da Yarima Harry sai tattaba kunne masu yawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel