Hotuna: Yadda Biloniyoyi Dangote da Tony Elumelu Suka Dauka Hankalin Jama'a a Filin Jirgi

Hotuna: Yadda Biloniyoyi Dangote da Tony Elumelu Suka Dauka Hankalin Jama'a a Filin Jirgi

  • Haduwar manyan 'yan kasuwar Afrika, Aliko Dangote da Tony Elumelu shugaban UBA da Transcorp Group sun dauka hankali
  • manyan 'yan kasuwan sun ci karo da juna a filin jirgin sama na Legas a ranar Laraba inda suka kashe hannaye tare da gaisawa
  • A hotunan da Elumelu ya wallafa, yace sun ci karo da Aliko Dangote wanda ya kira da Alicash a ranar Laraba a Legas

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Legas - Haduwar manyan masu kudin Afrika, shugaban Dangote Group kuma bakar fata da yafi kowa arziki a duniya, Aliko Dangote da shugaban bankin UBA da Transcorp Group, Tony Elumelu ta matukar kayatarwa.

Manyan 'yan kasuwan sun ci karo da juna a filin sauka da tashin jiragen sama a ranar Laraba.

Dangote and Elumelu
Hotuna: Yadda Biloniyoyi Dangote da Tony Elumelu Suka Dauka Hankalin Jama'a a Filin Jirgi. Hoto daga @tonyoelumelu
Asali: Instagram

Manyan masu kudin 'yan Najeriya da ke da hannayen jari a fannin kasuwanci, nishadi da sauran bangarori a Afrika sun sha hannnu tare da bayyana suna murmushi yayin da aka dinga kyasta musu hotuna.

Kara karanta wannan

Jerin Mutanen Da Tukur Mamu Ya Yi Sanadiyyar Kubutarsu Daga Hannun 'Yan Bindiga

Elumelu wanda ya wallafa hotunan gamuwarsu a shafinsa na Instagrma, ya yi tsokaci da:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Laraba ce mai zafin rana a Legas tare da Alicash!"

Kano: Masu Fadi a Ji Sun Dira Auren Diyar Sarki Aminu Bayero da 'Dan Sarkin Kibiya

A wani labari na daban, kwaryar birinin Kano ta cika ta batse a ranar Juma'a yayin da 'dan sarkin Kibiya, Alhaji Umar Usman ya auri diyar Sarkin Kano, Rukayya Aminu Bayero inda manyan mutane suka halarci daurin auren.

Jim kadan bayan addu'o'in, Dr Abdullahi Umar Ganduje wanda ya tsaya matsayin waliyyin amarya, yayi addu'ar Allah ya albarkaci auren tare da basu yara nagari.

An daura auren a fadar Sarkin Kano tare da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje wanda ya bayar da auren kan sadaki N200,000.

Babban limamin jihar Kano, Farfesa Sani Zahradeen ya yi addu'a ga ma'auratan tare da shawartarsu da su zauna cikin lumana da kwanciyar hankali.

Kara karanta wannan

Mutum 43 Da Aka Sace A Masallacin A Zamfara Sun Samu Kubuta Bayan Biya Kudi, Daya Ya Mutu

Asali: Legit.ng

Online view pixel