Bidiyon Fitacciyar 'Yar TikTok Tana Cashewa a Masallaci, 'Yan Sanda Sun Kama ta

Bidiyon Fitacciyar 'Yar TikTok Tana Cashewa a Masallaci, 'Yan Sanda Sun Kama ta

  • Bidiyon wata budurwa 'yar kasar Pakistan ya yadu inda aka ganta tana kwasar rawa a TikTok cikin Masallaci
  • An ga budurwar ta shiga cikin Masallacin babu dankwali da kuma shigar da bata dace ba, inda sauran masu daukar bidiyon ke biye da ita
  • Tuni 'yan sanda suka yi ram da ita bayan shugaban Masallacin ya kai korafin wulankanci da rashin mutunta wurin bautar da tayi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Islamabad, Pakistan - 'Yan sanda a ranar Litinin sun damke wata fitacciyar 'yar TikTok da mukarrabnata bayan bidiyon da suka yi a Masallacin Faisal ya yadu a kafafen sada zumuntar zamani.

A martanin wani korafi da Mohsin Ishaq ya shigar. wanda shine Limamin masallacin, a kan mai TikTok din da ma'aikatanta da suka hada da mai daukar hoto, ya mika karar ofishin 'yan sandan Margalla a karkashin PPC 295-A.

Kara karanta wannan

Wani Matashi Ya Koma Jami'ar Da Yayi Karatu, Yace Su Bashi Kudinsa Su Karbi Kwalinsu

TikToker
Bidiyon Fitacciyar 'Yar TikTok Tana Cashewa a Masallaci, 'Yan Sanda Sun Kama ta. Hoto daga theislamicinformation.com
Asali: UGC

The Islamic Information sun rahoto cewa, a korafinsa, ya kwatanta bidiyon da ya yadu a soshiyal midiya matsayin rashin mutunta addinin da wurin bautar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An ga matar ta shiga masallacin babu dankwali a kanta da kuma shigar da bata dace ba. Daga nan cike da isa tare da tunkaho ta fito farfajiyar Masallacin Faisal din.

Kamar yadda FIR tace, tunda shugaban masallacin Musulmi ne kuma 'dan kasar Pakistan, hakan ya matukar bata masa rai inda suka kara da cewa an bayyana rashin mutunta addinin a soshiyal midiya kuma TikTok tana neman zama tamkar wani abu mai muhimmanci a tsakanin matasa.

Kamar yadda FIR tace, hakkinmu ne na dole ganin bayan ire-iren wadannan abubuwan a tsakanin matasa.

Bayan mika korafin, 'yan sanda sun fara bincike kuma sassan da suka dace sun tintuba tare da gano budurwa da sauran wadanda ake zargin inda har da asusun TikTok din ta aka gano.

Kara karanta wannan

Na Gaji da Najeriya Ne: Yaro Mai Shekaru 14 da Aka Tsinta a Filin Jirgin Sama

Alkali Ya Aika Matashi Gidan Yari Bayan Ya Watsawa 'Yar Sanda Najasa

A wani labari na daban, wata kotun gargajiya mai daraja ta daya dake Ibadan jihar Oyo, a ranar Litinin ta yankewa matashi mai shekaru 23 mai suna Abayomi Damilare hukuncin zaman gidan maza na wata shida bayan ya watsawa ‘yar sanda kashi.

Alkalin kotun ta yankewa matashin wannan hukuncin bayan ya amsa laifinsa tare da shaidu gamsassu da aka mikawa kotun.

Akintayo a takaice ta yi shari’a tare da yankewa matashin hukuncin wata shida a gidan yari da aiki mai wahala.

Asali: Legit.ng

Online view pixel