Budurwa ta sha da kyar a hannun danginta bayan ta haifo balaraben jariri bayan ta dawo daga Saudiyya
- Anna Awuor ta bar kasarta inda ta tafi Saudi Arabia domin samowa ya'yanta abinci amma ta kare da fadawa hannun mugun ubangida
- Ubangidanta ya dinga cin zarafinta har ta samu ciki, bayan ya gane tana dauke da cikinsa, yasa aka wurgota kasarta
- 'Yan uwanta dake Siaya a Kenya basu sassauta mata ba, sun fatattaketa bayan ta haifo balaraben jariri bayan dawowarta
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Masoyan wata mata a Kenya sun taimaketa bayan 'yan uwanta dake Siaya sun fatattake ta sakamakon haihuwar balaraben jariri da tayi bayan ta dawo daga Saudiyya.
Anna Awuor mai shekaru 29 a duniya ta shiga wani hali bayan danginta sun gujeta tare da jaririn da ta haifa bayan ta dawo daga Saudi Arabia
Kamar yadda mai taimakon jama'a, Judy Oricho ta bada labarin halin da matar ta shiga a shafinta na Facebook, ubangidan Anna na Saudi Arabia ne ya ci zarafinta kuma sakamakon hakan ta samu juna biyu.
Matar Marigayi Alaafin Na Oyo Ta Dawo Daga Saudiyya Kawai Sai Ta Tarar Da Kyautar Mota Daga Wani Bawan Allah
Bayan ya gane zata haihu, ya sa aka dawo da ita Kenya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Daga bisani ta haihu kuma iyayenta sun fatattaketa tare da 'ya'yanta saboda balaraben da ta Haifa," Oricho ta bada labari.
Bayan an koreta daga gida, ta je Migori wurin wasu danginta domin neman mafaka amma ta tarar sun tashi. Daga nan ne ta tafi sansanin sarki dake Migori don neman taimako.
"Tana bukatar kowanne irin taimako daga wurinku, abinci, kayan sanyawa da kuma wurin kwana tare da yaranta," Oricho ta rubuta.
Cike da sa'a, masu taimako a kasar sun kadu da jin halin da ta shiga kuma wata kungiya ta gaggauta kai mata dauki.
"Nagode, ina farin cikin sanar muku cewa kungiyar harvest of hope Africa ta kawowa Anna dauki kuma ta karbeta tare da yaranta," Oricho tace.
An yi wa amarya da angon da suka rasu shekaru 30 da suka wuce bikin kece-raini a Indiya
A wani labari na daban, wata amarya da angonta da suka rasa rayukansu shekaru 30 da suka gabata sun yi aure a wani gagarumin bikin kece-raini wanda ya samu halartar 'yan uwansu da abokan arziki a Indiya.
Wani ma'abocin amfani da Twitter 'dan kasar Indiya mai suna @anny_arun ne ya bada labarin yadda auren ya kasance.
Ya yi bayanin cewa, a al'adarsu idan mutum ya mutu yana karami, iyalan mamacin na iya nemo wani wanda ya rasu yana karami ta yadda za a yi musu aure.
Asali: Legit.ng