Bidiyo: Sabuwar budurwa dalleliya zan auro daga Isra'ila, Jarumin fim mai shekaru 71

Bidiyo: Sabuwar budurwa dalleliya zan auro daga Isra'ila, Jarumin fim mai shekaru 71

  • Jarumin masana'antar fina-finai mai shekaru 71, Kenneth Aguba, yace budurwa sabuwa dal yake son aure daga Isra'ila
  • A cewar jarumin da cikin kwanakin nan wani fasto ya tsamo shi daga talauci inda ya bashi gida, yace dole budurwar ta kasance doguwa siririya
  • Ya kara da cewa, shi ba 'dan kabilar Ibo bane kuma ba 'dan Najeriya ba, shi asalinsa 'dan kasar Isra'ila ne

Tsohon jarumin masana'antar fina-finai ta Nollywood, Kenneth Aguba ya cigaba da bayyana tsayuwarsa tsayin daka a dangane da hukuncinsa na auren sabuwar budurwa dal daga Isra'ila.

Idan za a tuna, jarumin wanda bashi da ko gidan kansa a baya, ya samu taimako daga babban faston Omega Power Ministries, Apostle Chibuzor Chinyere wanda ya bashi gida yayin da yake ciyar da shi.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Wata Amarya Da Mahaifinta Suka Fashe Da Kuka A Wajen Liyafar Bikinta

Kenneth Aguba
Bidiyo: Sabuwar budurwa dalleliya zan auro daga Isra'ila, Jarumin fim mai shekaru 71. Hoto daga Lucky Udu
Asali: UGC

Apostle Chibuzor ya bayyana cewa zai sanarwa da Aguba mata kuma lokacin da wata budurwa ta bayyana cewa tana kaunarsa, yace baya son ta inda ya tabbatar da cewa budurwa yake so daga Isra'ila, lamarin da ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani.

Sai dai a wata tattaunawa da yayi da Lucky Udu, Aguba ya kara bayyana wani lamari mai bada mamaki game da tsatsonsa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A yayin da aka tambaye shi ko yana son yin aure, yace eh yana bukatar mata amma ba da gaggawa ba.

A bidiyon, mai tambayar shi ya cigaba da tambaya idan yana da wata budurwa da yake so, ya tabbatar da hakan inda yace tana Isra'ila.

Kamar yadda tsohon jarumin ya fada, shi ba mutumin kabilar Ibo bane ko kuma 'dan Najeriya, amma tsatsonsa Isra'ila ne.

Kara karanta wannan

El-Rufai: Na Fadawa Tinubu Ban Bukatar Komai a Gwamnatinsa, Na Bada Dalilina

Ya cigaba da jaddada cewa, shi fa budurwa sabuwa dal yake so daga Isra'ila, doguwa kuma siririya.

Tantancewa nake yi, har yanzu ban ga nagartaccen namijin da ya dace da ni ba, Jarumar fim mai shekaru 52

A wani labari na daban, fitacciyar jarumar masana'antar Nollywood, Bimbo Akinsanya wacce aurenta ya mutu lokacin tana da yaro mai wata uku a shekarun baya da suka gabata, tace ta mayar da hankali kan fim a yanzu fiye da batun aure.

A tattaunawarta da jaridar Vanguard, tace tana kokarin ganin ta bai wa 'danta lokacinta wanda hakan ke da matukar muhimmanci.

Ta bayyana yadda take kula da 'danta ita kadai ba tare da tallafin uban yaron ba. "Ba abun wasa bane kula da 'da kai kadai babu wani tallafi. Tunda na rabu da mahaifinsa, ban taba samun wani tallafi na kula da yaron ba har yanzu."

Kara karanta wannan

Buhari: Mun Ba Wa Jami'an Tsaro Cikakken 'Yanci Su Kawo Karshen Ta'addanci

Asali: Legit.ng

Online view pixel