Abun mamaki: Yadda Giwa ta halaka wata mata, ta bi ta wurin jana'izarta ta tattake gawar

Abun mamaki: Yadda Giwa ta halaka wata mata, ta bi ta wurin jana'izarta ta tattake gawar

  • Wata giwa ta halaka wata tsohuwa mai shekaru 70 a duniya inda ta tattaketa yayin da take tara ruwa a kauyen Raipal dake Indiya
  • Tsohuwar ta samu miyagun raunika wanda yasa aka garzaya da ita asibiti inda tace ga garinku duk a ranar
  • Da yammacin ranar, 'yan uwanta sun fara mata jana'iza amma Giwar ta sake bayyana kuma ta tattaketa gawar tsohuwar tare da arcewa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wani abun mamaki ya faru a kauyen Raipal dake Indiya inda wata katuwar giwa ta halaka wata tsohuwa mai shekaru 70 kuma ta je har inda ake jana'izar tsohuwar tare da tattake gawar.

Giwar ta arce bayan da ta halaka matar yayin da take tara ruwa a kauyen Raipal. An garzaya da tsohuwar asibiti inda tace ga garinku sakamakon miyagun raunikan da ta ji, Aminiya ta rahoto.

Kara karanta wannan

Bidiyon Wata Budurwa Yayin Da Ta Yi Cikibis Da Matar Da Ta Raine Ta Bayan Shekaru 25

Ba a nan Giwar ta hakura ba, ana tsaka da jana'izar tsohuwar da yammacin ranar, sai Giwa ta sake bayyana kuma ta je ta tattake gawarta daidai lokacin da danginta ke mata addu'o'i.

Giwa ta kashe wata mata
Abun mamaki: Yadda Giwa ta halaka wata mata, ta bi ta wurin jana'izarta ta tattake gawar. Hoto daga aminiya.dailytrust.com
Asali: UGC

Bayan Giwar ta tafi, 'yan uwan tsohuwar sun cigaba da jana'izar. Majiyoyi sun tabbatar da cewa, Giwar ta arce daga cikin namun daji dake garin Mayurbhanj dake da nisan kilomita 200.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A watan Oktoban shekarar da ta gabata, rahotanni sun bayyana yadda wata giwa ta take wani tsohon da ya je yawon bude-ido inda ta halaka shi har lahira a kasar Zimbabwe.

Tsohon mai suna Michael Walsh yana da shekaru 71 a duniya kuma tare yake da 'dansa mai shekaru 41 lokacin da suke tafiya a safiyar cikin dajin yankin da aka killace namun daji Mana Pools National Park.

Kara karanta wannan

Bidiyon doguwar budurwa mai shekaru 22, tana da tsayin ban mamaki

Cike da tashin hankali, matashi ya sanar da mutuwar budurwar da zai aura nan da sati 2

A wani labari na daban, rashin masoyi babban ibtila'i ne da kan fadawa 'dan Adam, sau da yawa a kan dade ana jinyar zuciya idan ta rasa abinda take so balle a ce mutuwa ce ta gifta.

Wani matashi mai suna Safiyanu Abubakar ya wallafa katin bikinsa wanda za a yi a ranar 12 ga watan Augutan 2022 da masoyiyarsa Rukaiya Ibrahim Salihu.

Matashin ya bayyana sanarwar mutuwar budurwarsa wacce zasu angwance tare nan da makonni biyu cike da damuwa a shafinsa na Twitter mai suna @SufyToro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel