Bidiyon Wata Budurwa Yayin Da Ta Yi Cikibis Da Matar Da Ta Raine Ta Bayan Shekaru 25

Bidiyon Wata Budurwa Yayin Da Ta Yi Cikibis Da Matar Da Ta Raine Ta Bayan Shekaru 25

  • Wata Baturiya ta sake haduwa da wata dattijuwar mata bakar fata wacce ta raine ta a lokacin da take karama
  • Tsawon shekaru 25 rabon da su hada ido da juna kawai sai gashi sun yi kicibis da junansu a wani shagon siyayya
  • A cikin wani bidiyo da ya yadu a yanar gizo, an gano mutanen biyu runjume da junansu cike da kauna

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wata kyakkyawar matashiyar budurwa farar fata ta sake haduwa da mai rainonta wacce suka rabu tsawon shekaru 25 da suka shige.

Rahotanni da aka samu sun nuna cewa dattijuwar matar ta taimaka wajen kula da budurwar wacce take baturiya a lokacin da take yar karamar yarinya.

Budurwa da mai aiki
Bidiyon Wata Budurwa Yayin Da Ta Yi Cikibis Da Matar da ta Raine Ta Bayan Shekaru 25 Hoto: @eddie4356
Asali: UGC

Sai dai kuma, sun rasa lambobin wayar junansu sannan tsawon shekaru 25, basu sake sanya junansu a ido ba.

Kawai sai gashi sun taki sa’a, baturiyar ta hango matar a wani shagon sayayya kawai sai ta tunkare ta.

Kara karanta wannan

Bidiyon doguwar budurwa mai shekaru 22, tana da tsayin ban mamaki

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da farko, Mai rainon nata bata gane ta ba amma bayan wasu yan sakwanni, sai ta tuna fuskarta, sannan ta rungumeta sosai. @eddie4356 ce ta wallafa bidiyon a shafin TikTok.

Bidiyon ya janyo martani

@susanmariecovel tace:

“Wayyo Allah soyayyar uwa da ta sake haduwa da danta ta taba gashinki don tabbatar da cewar da gaske ne nan take na fashe da kuka.”

@jilliebulian72 ta yi martani:

“Ta taba gashin kanki wanda ke nuna tana alfahari da yadda kika zama cikakkiyar budurwa a yanzu.”

@mosthighlevel1 ta ce:

“Ma shaa Allah abun ya taba zuciya za ka iya gane cewa ta dauke ta kamar diyar da ta haifa.”

Kalli bidiyon a kasa:

Bidiyon Bikin Zagayowar Ranar Haihuwar Tsohon Sarkin Kano, Sanusi, An Yanka Kek

A wani labarin, bidiyon bikin zagayowar ranar haihuwar tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi Lamido ya bayyana a shafukan soshiyal midiya.

Kara karanta wannan

Yadda Malamar Jami’a Ta Koma Tallan Dankali Saboda Yajin Aikin ASUU

A ranar Lahadi, 31 ga watan Yuli ne Sanusi II ya cika shekaru 61 a duniya inda aka yi shagali na musamman domin raya wannan rana.

A cikin bidiyon shagalin wanda shafin hausaa_fulanii ya wallafa a Instagram, an gano tsohon sarkin wanda ake yiwa lakabi da Dawisu sarkin ado tsaye cikin ado da kwalliya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel