Magidanci ya cinye akuya 1, 2Kg na shinkafa da donot 40 a zama daya, matarsa ta tsere
- Saidi Msosi daga kasar Tanzania ya ba kowa mamaki ta yadda ya cinye akuya 1 da shinkafa 2kg da donot 40 a zama daya tak
- Matarsa masoyiyarsa tserewa tayi ta bar shi ganin irin wannan dabi'ar kuma tayi ikirarin cewa ta gaji da shirga masa abinci yana lamushewa
- Msosi, wanda cikinsa ba irin na mutane bane, ya samu kudade masu tarin yawa daga gasar cin abinci kuma ya samu fuloti, gida da babura biyu
Wani mutum 'dan kasar Tanzania ya iya cinye 2kg na shinkafa da akuya daya a zama daya. Ya sanar da cewa matarsa ta gudu ta bar shi saboda tsabar cin abincinsa.
Msosi ya yi nasarar lashe gasar cin abinci ta Tonge nyama. Saidi Msosi, wanda yayi nasarar lashe gasar cin abinci ta Tonge nyama a Morogoro, ya bar mutane baki bude saboda yadda ya cinye donot 40 a cikin minti 20 kacal.
A wata tattaunawa da Millard Ago, Msosi yace ya ziyarci likita kuma an sanar masa cewa hana da katon ciki ba kamar na sauran mutane ba kuma ya cigaba da cin abincinsa.
"Na cinye donot 40 a cikin minti 20 kacal. Na fara cin kwano uku zuwa hudu har na kai ga mataki babba," Msosi yace.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Naje an duba ni kuma aka sanar min cewa cikina babba ne," ya kara da cewa.
Matarsa ta tsere
Matarsa ta tsere zuwa wasu tsaunika bayan ta ga yadda mijin ta ya ci abincin kuma ta gaji da dafa abinci mai yawa.
A gidansa, yana ci 3kg na shinkafa da kaza biyu a zama daya a kowacce rana.
"Bani da mata, ina hayar mata ne su yi min girki in biya su. A yanzu, bani da aure, bana bukatar wata mata," Msosi yace.
A yanzu, zai iya cinye 10kg na shinkafa da akuya daya a zama daya.
Msosi ya yi nasara a gasar cin abinci
Msosi ya yi nasarar cin gasa daban-daban na cin abinci wanda a haka ya siya fuloti, ya gina gida duk da kudin. Ya mallaki babura biyu saboda gasar da yake ci.
Msosi wanda ke da nauyin 72kg ya musanta zargin da ake masa kan cewa yana amfani da maita wurin cin gasar.
Magidanci yayi shagalin sallarsa da matansa 3 da 'ya'ya 19, hotunansu sun janyo cece-kuce
A wani labari na daban, wani 'dan Najeriya yayi shagalin bikin sallah babba inda har ya bayyana hotunansa tare da matansa uku reras da 'ya'yansa 19.
Bawan Allah mai suna Baba Lawal, ya wallafa kyawawan hotunan ne a ranar Lahadi, 10 ga watan Yulin 2022 a shafinsa na Facebook.
Asali: Legit.ng